Yanzun Nan: Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto

Yanzun Nan: Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto

  • Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi Alla wadai da rikicin da ya jawo kisan ɗalibar da ake zargi da ɓatanci a Sokoto
  • Buhari ya ce musulman duniya na girmama dukkan Annabawan Allah, amma ba kyau ɗaukar doka a hannu
  • A madadin ƙasa baki ɗaya, Buhari ya miƙa ta'aziyya ga iyalan matashiyar da aka kashe a rikicin

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi Alla-Wadai da ɗaukar doka a hannu da wasu matasa suka yi a Sokoto, wanda ya yi sanadin ta da yamutsi da kashe ɗalibar Kwalejin Shehu Shagari, Deborah Samuel, bisa zargin ta zagi Annabi Muhammad (SAW).

Buhari yace labarin kashe matashiyar yarinyar da ɗalibai yan uwanta suka yi abun damuwa ne, kuma ya bukaci a gudanar da bincike a tsanake kan abin da ya haddasa kafin da lokacin lamarin.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

Shugaba Buhari a rahoton TVC News, ya ce Musulmai a faɗin duniya na girmama Manzannin Allah, da suka haɗa da Annabi Isah (AS) da Annabi Muhammad (SAW).

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Yanzun Nan: Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Sai dai a cewar Buhari, duk inda ka samu wani ya yi zalunci kamar yadda ake zargin ya auku a Sokoto, doka ba ta yadda kowa ya ɗauki mataki da hannu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kasan yace:

"Shugabannin addini sun faɗa mana ba dai-dai bane mabiyi ya yanke hukunci kan aikin da wani mutum ya yi, wajibi a bar hukumomi su ɗauki mataki kan irin haka idan ta taso."
"Babu wani mutum da ke da ikon ɗaukar doka a hannunsa a ƙasar nan saboda haka ta da zaune tsaye ba zai taɓa magance ko wace irin matsala ba ce."

Bayan haka Buhari ya umarci ma'aikatar yaɗa labarai da al'adu, hukumar jin daɗin yan sanda, da ma'aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani su yi aiki da kamfanonin sadarwa domin daƙile yaɗa bayanan ƙarya ta kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Sokoto: Mutane sun mamaye tituna da zanga-zanga, sun nemi a saki waɗan da suka kashe ɗalibar da ta zagi Annabi

Buhari ya jajantawa iyalan ɗalibar da aka kashe

Bugu da ƙari, Buhari a madadin ƙasa ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan dalibar da aƙa ƙashe tare da fatan samun lafiya cikin sauri ga waɗan da suka jikkata.

Shugaban ya yaba da saurin ɗaukar matakin gwamnati kuma ya roki Malumma su dawo da mutane cikin hayyacin su game da yancin magana.

A wani labarin na daban kuma bayan gana wa da Buhari Ministan Kwadugo, Chris Ngige, ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2023

A wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu, Ngige ya ce ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazari da kuma neman shawari wurin makusanta.

A cewarsa hakan zai ba shi cikakkiyar damar maida hankali kan aikinsa da taimaka wa shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel