Zaɓen 2023: Kada Ka Ruɗa Ƴan Najeriya, Ƙungiya Ta Ja Kunnen Atiku

Zaɓen 2023: Kada Ka Ruɗa Ƴan Najeriya, Ƙungiya Ta Ja Kunnen Atiku

  • An ja kunnen tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar akan kin tsayar da magana dangane da matakin da dattawan arewa suka dauka akan 2023
  • Kungiyar Dattawan Arewa wacce Fafesa Ango Abdullahi ya ke shugabanta ta zabi mutane 2 cikin ‘yan takara 4 da suka gabatar da kawunansu domin sasanci
  • Sai dai Atiku ya ki amincewa da batun zaben tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed bayan kammala sasancin

Kaduna - Wata kugiyar mai suna, Generational Powershift Forum, GPF, ta ja kunnen tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar akan surutai dangane da yiwuwar tsayar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Sarki ko kuma gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed na jam’iyyar PDP a arewa.

Legit.ng ta ruwaito yadda shugaban kungiyar na kasa, Ibrahim Abdullahi ya saki wannan sanarwar a ranar Asabar, 23 ga watan Afirilu, inda ya ce yayin da dattawan da kuma sauran kungiyoyi ke zaben mutanen Atiku bai gabatar da kansa ba.

Kara karanta wannan

Ku yi koyi da Dangote: Buhari ya ba 'yan kasuwan Najeriya shawari mai ban mamaki

Shugabancin 2023: Kada Ka Ruda 'Yan Najeriya, Wata Kungiya Ta Ja Kunnen Atiku
Shugabancin 2023: Kaɗa Ka Ruda 'Yan Najeriya, Wata Kungiya Ta Gargadi Atiku
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa, yanzu tarihi ya fi mara wa ‘yan siyasa masu karancin shekaru baya, inda ya ce alamun za a samu sauyi daga tsohuwar siyasa zuwa sabuwa sun bayyana.

Abdullahi ya shawarci Wazirin Adamawa da ya dena nuna rashin amincewarsa da sakamakon sandancin da bai gabatar da kansa don a yi ba. Kasancewar yanzu ana bukatar sauya salon mulki a 2023.

Takardar ta yi kira ga Atiku akan shiga cikin tafiyar samar da canji da kuma karba-karba a PDP, inda ta ce ya bar sabbin hannu su amshi mulki.

Cikin ‘yan takarar da suka gabatar da kawunansu don sasancin akwai Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Bala Mohammed, Saraki da Mohammed Hayatu-Deen.

Sai dai daga baya aka fitar da sakamakon wanda kwamitin sasancin na musamman wanda Farfesa Ango Abdullahi ya shugabanta, ta gabatar da sakamakon gaban tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida.

Kara karanta wannan

Dole ka tsaya takara: Masoya Jonathan sun mamaye ofishinsa, suna neman gafara

Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP

A wani labarin, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya bai halarci taron sirrn da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya ba tare da wasu ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ba, yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke karatowa.

An tattaro yadda ‘yan takarar suka dade suna tattaunawa dangane da wanda zai tsaya takara don gudun tashin tarzoma ta cikin jam’iyyar yayin zaben, The Nation ta ruwaito.

‘Yan takarar da suka halarci taron da aka yi gidan gwamnati da ke Port Harcourt sun hada da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon manajan darekta na bankin kasa da kasa na FSB, Dr. Mohammed Hayatu-Deen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel