Ku yi koyi da Dangote: Buhari ya ba 'yan kasuwan Najeriya shawari mai ban mamaki

Ku yi koyi da Dangote: Buhari ya ba 'yan kasuwan Najeriya shawari mai ban mamaki

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da wani muhimmin sako ga shugabanni kuma jiga-jigan 'yan kasuwan Najeriya
  • Shugaban kasan ta bakin mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya bukaci 'yan kasuwa da su yi koyi da hamshakin attajirin Afrika, Aliko Dangote
  • Buhari wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a ya bukaci ‘yan kasuwa da su saka hannun jari a fannoni daban-daban da za su kawo ci gaban tattalin arzikin kasar nan

FCT, Abuja - A ranar Juma’a, 22 ga watan Afrilu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci ‘yan kasuwa da su rika amfani da dabaru don habaka fannonin tattalin arziki, tare da yin tasiri mai tsawo wajen samar da ayyukan yi da rage radadin talauci.

Kara karanta wannan

Abin da Shugaban kasa ya fadawa Malamai da Sarakuna da suka yi buda-baki a Aso Villa

Ya ba da wannan sahwara ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban rukunin masana'antun Dangote, Aliko Dangote da mambobin rukunin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shawarin Buhari ga 'yan kasuwan Najeriya
Ku yi koyi da Dangote: Buhari ya yi kira ga jiga-jigan 'yan kasuwan Najeriya | Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Femi Adesina ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, ta wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Legit.ng Hausa ta samo daga shafinsa na Facebook.

Shugaban ya ce kalubalen harkokin sufuri da makamashi za su ci gaba da jan hankalin jama’a a kasar nan.

Saboda haka, shugaban ya bukaci ‘yan kasuwa a kasar da masu zuba jari da su mai da hankali kan bangarorin da za su amfani kasa tare da kawo ci gaba

Buhari ya kuma ba da tabbacin cewa inganta ababen more rayuwa shi ne babban abin da gwamnati ta mayar da hankali akai.

Kara karanta wannan

Sabon nadi: Buhari ya nada mai taimaka masa kan samar da ayyukan yi ga 'yan Najeriya

Shugaba Buhari dai ya sha nanata manufar gwamnatinsa ta inganta 'yan kasa, yaki da rashawa, samar da ayyukan yi da sauransu.

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin wasu jiga-jigai daga masana'antar Dangote

A tun farko kun ji cewa, a yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da wasu jiga-jigai daga rukunin masa'anatun Dangote a fadarsa da ke Abuja.

Legit.ng Hausa ta samo labarin ne yayin da hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Buhari Sallau ya yada wasu hotuna na ganawar ta shafinsa na Twitter.

Hotunan da ya yada suna dauke da rubutu kamar haka: "Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin kwamitin gudanarwa ta rukunin masana'antun Dangote a fadar shugaban kasa a yau Laraba 22 ga watan Afrilu 2022."

Asali: Legit.ng

Online view pixel