Duk masu sukar shugaba Buhari suna da hannu a ta'addancin yan bindiga, Gwamna Uzodinma

Duk masu sukar shugaba Buhari suna da hannu a ta'addancin yan bindiga, Gwamna Uzodinma

  • Gwamna Uzodinma na jihar Imo ya ɗora ayar tambaya kan masu ganin laifin shugaba Buhari game da taɓarɓarewar tsaro
  • Gwamnan ya ce duk masu sukar shugaban kasa kan halin da ake ciki to da alama suna taimaka wa yan bindiga ta wata hanya
  • Mista Hope Uzodinma ya kuma fallasa yan siyasan da yake zargin suna rura wutar matsalar tsaron jiharsa ta Imo

Imo - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ƙi yarda da masu zargin cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kamata a ɗora wa laifin taɓarɓarewar tsaro a Imo.

Gwamnan ya bayyana cewa duk masu kalar wannan tunanin da alamu suna da hannu ta karkashin kasa a ayyukan yan bindiga, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Uzodinma ya kuma ankarar da cewa a halin yanzun mambobin APC a Imo sun koma abun harin wasu yan siyasa da abokan haɗin guiwarsu, waɗan da ke taimakawa yan bindiga da masu kisan kai.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari tayi magana a kan ceto Bayin Allah da aka sace a jirgin Kaduna-Abuja

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.
Duk masu sukar shugaba Buhari suna da hannu a ta'addancin yan bindiga, Gwamna Uzodinma Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wurin ɗaura auren ɗan fitaccen ɗan kasuwan nan kuma ɗan siyasa, Emmanuel Iwuanyanwu, wanda ya gudana a wata Coci dake Owerri ranar Litinin.

Ya ce sheɗanun yan siyasa sun kuduri aniyar lalata jihar Imo ta hanyar kashe mutane haka nan, da kuma ƙona kayan gwamnati da masu zaman kansu kuma duk da sunan siyasa.

Ya roki Cocin da sauran taron mutane su cigaba da sa irin waɗan nan mutane a addu'o'insu ko Allah zai sa su tuba.

Tsaron Imo na da alaƙa da siyasa - Uzodinma

Da yake a jawabi a gaban taron Jama'a a wata Coci a ƙaramar hukumar Oru ta gabas, tun ranar Lahadi, Uzodinma ya ce ƙashe-kashen dake faruwa na da alaƙa da siyasa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun kai mummunan hari garin su gwamnan jiha, sun tafka ɓarna

Ya ce:

"Ina fatan shiriyar Allah ta shiga zuciyar mutanen dake taimaka wa wajen ƙashe-kashen mutane, ƙona gidaje da lalata kadarorin gwamnati duk da sunan siyasa."

A wani labarin kuma Yan bindiga sun harbe Fitaccen ɗan kasuwa har Lahira a gaban Budurwar da zai Aura mako mai zuwa

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun harbe wani babban ɗan kasuwa a jihar Ebonyi mako ɗaya kafin ɗaura aurensa.

Bayanai sun nuna cewa makasan sun halaka mutumin mai suna Chukwu a gaban matar da zai aura, suka kwace mata waya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel