Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai hari kauyen su gwamna, sun buɗe wa yan sanda wuta

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai hari kauyen su gwamna, sun buɗe wa yan sanda wuta

  • Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Isuofia dake ƙaramar hukumar Aguata, inda gwamnan Anambra mai ci ya fito
  • Majiya daga yankin ta taabbatar da cewa harin ya yi muni, kuma yan bindigan sun halaka jami'in ɗan sanda guda ɗaya
  • Amma a cewar hukumar yan sanda ta Anambra, dakarunta uku ne suka ji raunuka amma babu wanda ya mutu

Anambra - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an bindige ɗan sanda har lahira a ƙauyen Isuofia, ƙaramar hukumar Aguata, jihar Anambra.

Yankin Isuofia a Aguata, nan ne gwamnan jihar Anambra mai ci wanda ya karɓi ragamar mulki a watan Maris, Farfesa Charles Soludo, ya fito.

A cewar wata majiya daga yankin, yan bindigan sun farmaki wata mahaɗar hanyoyi, inda jami'an tsaro suka kafa madakata kuma suka buɗe musu wuta.

Kara karanta wannan

NBS: Tsadar biredi, gas da mai sun jawo tashin farashin sauran kayayyaki a Najeriya

Yan bindiga sun kai hari Anambra.
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai hari kauyen su gwamna, sun buɗe wa yan sanda wuta Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Haka nan, majiyar ta yi ikirarin cewa yan bindigan sun fusata da matakin girke jami'an tsaro a wurin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce:

"Yan bindigan sun shiga yankin, suka bude wuta kan mai uwa da wabi ba tare da jinkirta wa ba, yayin da mutane suka yi takansu domin tsira da rayuwarsu. Ɗan sanda guda ɗaya ya mutu a harin."

Ba'a kashe ko mutum ɗaya ba - Yan sanda

Kakakin rundunar yan sanda ta jihar Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da faruwar kai harin amma ya musanta kashe ɗan sanda ɗaya.

Kazalika kakakin yan sandan ya ce ba cikin ƙauyen aka aka kai hari ba, lamarin ya faru ne a kan hanyar wucewar ababen hawa.

Ya kuma bayyana cewa yayin harin wanda dakarun yan sanda suka yi musayar wuta da maharan, mutum uku ne suka jikkata daga cikin jami'an.

Kara karanta wannan

Mun cika alkawuran da muka yiwa yan Najeriya a dukkan bangarori, musamman gidaje: Buhari

DSP Tochukwu yace dakaru sun kwato mota ɗaya daga hannun maharan, sun ga jini a jikinta, alamar da ke nuna cewa an ɓarnata wasu daga cikkn maharan.

Amma majiya daga yankin ta jaddada cewa harin ya auku a kauyen Isuofia, kuma ɗan sanda ɗaya ya rasa rayuwarsa, kamar yadda Tribune ta rahoto.

A wani labarin na daban kuma Matawalle ya rantse da Alkur'ani, ya fallasa wasu manyan mutane dake taimaka wa yan bindiga a Zamfara

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce akwai sa hannun wasu masu faɗa aji na jihar a taɓarɓarewar tsaro.

Bisa haka gwamnan ya rantse da Alƙur'ani kuma ya ƙalubalanci sauran shugabannin siyasa su rantse dan kauce wa zargi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel