'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Gidan Ɗan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar APC Kwana 4 Bayan Sanar Da Takararsa

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Gidan Ɗan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar APC Kwana 4 Bayan Sanar Da Takararsa

  • Tonye Princewill, dan takarar gwamnan Jihar Rivers ya zargi wasu ‘yan bindiga da kai wa gidansa farmaki sai dai basu sace wani abu mai tsada ba
  • Kamar yadda ya shaida, sun kai farmakin ne gidansa ne da ke GRA a Port Harcourt da safiyar Juma’a inda suka bincike dakin da suke zargin nashi ne
  • Harin ya biyo bayan kwana 4 da ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar a shekarar 2023 karkashin inuwar jam’iyyar APC

Rivers - Wani dan takarar gwamnan Jihar Rivers, Tonye Princewill ya zargi wasu ‘yan bindiga da ba san ko suwaye ba da afkawa gidansa amma ba su taba wani abu mai tsada ba, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, ‘yan bindigan sun kai hari gidansa da ke GRA a Port Harcourt da safiyar Juma’a inda suka bincike duk dakunan da suke zargin na dan takarar ne.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Gidan Ɗan Takarar Gwamna Kwana 4 Bayan Sanar Ƙudirinsa Na Yin Takara
'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Gidan Na Hannun Daman Amaechi Da Ke Son Gadon Kujerar Wike. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lamarin ya biyo bayan kwana hudu da Princewill ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar a zaben 2023 da ke karatowa karkashin jam’iyyar APC.

A cewarsa an yi yunkurin ganin bayansa ne

Yayin tabbatar da aukuwar lamarin, a wata takarda wacce Princewill ya saki ranar Juma’a ya kwatanta harin a matsayin yunkurin halaka shi.

Yayin da ya alakanta harin da zabe mai zuwa, ya ce ‘yan bindigan basu taba komai ba sai rakodar CCTV da suka sace wanda hakan ke nuna sun yi yunkurin ganin bayansa ne.

Kamar yadda takardar ta zo:

“Ina tabbatar muku da cewa da safiyar nan aka balle gidana. Alamu sun nuna cewa ni suka yi yunkurin halakawa saboda dakin da suke zargin nawa ne suka balle amma ba su gan ni ba.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda hudu har lahira

“Ba su dauki komai ba sai rakodar CCTV wanda hakan ke nuna ni kadai suka so halakawa. Amma muna godiya ga Ubangijin da ya kare ni.”

Ya zargi wasu ‘yan siyasa

Kamar yadda The Punch ta ruwaito, Princewill ya ci gaba da cewa:

“Hakan na nuna cewa rububin zaben 2023 ya fara matsowa kuma wasu suna iyakar iyawarsu don ganin sun samu mulki. A baya hakan ya yi aiki amma banda yanzu.”

Ya ce ko kadan bai razana da harin ba, zai kara kaimi wurin ganin ya kai inda yake son zuwa. Kuma ya yi fatan Ubangiji ya fallasa wadanda suka kai masa harin.

Yayin da ya bukaci addu’a daga jama’a, ya ce yanzu haka jami’an tsaro suna bincike akan harin kuma yana da tabbacin za su yi iyakar kokarinsu.

An Bindige Ma'aikacin INEC Har Lahira A Wurin Yi Wa Mutane Rajistan Zabe

A bangare guda, Yan bindiga sun halaka wani jami'in Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Kasa, INEC, mai suna Mr Nwokorie Anthony a Jihar Imo.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka hallaka wani, suka sace 'yarsa mai shekaru 15 a Zaria

Daily Trust ta rahoto cewa an bindiga jami'in ne yayin aikin cigaba da yi wa mutane rajistan katin zabe a karamar hukumar Uboma ta jihar.

A cewar baturen zaben jihar, Farfesa Emeka Ezeonu, an kashe Nwokorie ne a Nkwo Ihitte (PU 004) a mazabar Amakohia (RA 02) a karamar hukumar Ihitte Uboma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel