Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda hudu har lahira

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda hudu har lahira

  • Yan bindiga sun farmaki ofishin yan sanda a Atani, karamar hukumar Ogbaru ta jihar Anambra inda suka bindige jami’ai hudu da ke bakin aiki
  • Harda jami’ar yan sanda mace cikin wadanda aka hallaka a harin na yau Laraba, 13 ga watan Afrilu
  • Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar al’amarin inda ta ce ta tura karin jami’ai zuwa yankin da lamarin ya wakana

Anambra - Akalla jami’an yan sanda hudu aka bindige a wani mummunan hari da yan bindiga suka kai kan ofishin yan sanda na Atani da ke karamar hukumar Ogbaru ta jihar Anambra.

Daily Trust ta rahoto cewa yan bindigar sun kai harin ne a tsakar daren Laraba, 13 ga watan Afrilu.

A cewar wata majiya daga Atani, maharan sun isa yankin ne da misalin karfe 1:30 na tsakar daren Laraba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun halaka basarake da wasu mutum 24, sun sace babura a Benue

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda hudu har lahira
Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda hudu har lahira Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Majiyar ta bayyana cewa jami’an yan sanda hudu, ciki harda mace sun rasa rayukansu a harin.

Ana ta kai hare-hare kan ofishoshin yan sanda da sauran cibiyoyin gwamnati a jihar Anambra tun bayan da Farfesa Chukwuma Soludo ya karbi mulki a matsayin gwamna kimanin makonni uku da suka gabata.

Soludo ya sha bayar da tabbacin cewa wadanda ke kai hare-haren ba za su ci bulus ba.

Vanguard ta rahoto cewa kakakin yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar al'amarin.

Ya ce:

“Yan ta’addan sun zo da misalin karfe 1:00 na tsakar dare, abun takaici, jami’an yan sanda hudu sun rasa ransu.”

Ya ce da samun labarin harin, kwamishinan yan sanda, CP Echeng Echeng, ya gaggauta tura jami’an rundunar daga wurare daban-daban zuwa yankin.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe

A cewarsa, har zuwa lokacin da jami’an tsaro karkashin jagorancin kwamishinan yan sandan suka isa wajen, yan iskan na nan.

Ya ce:

“Mun fara binciken sirri kuma muna fatan gano mutanen da suka kai harin.”

Jami’an tsaro sun yi nasarar dakile wani hari kan kauyen Kaduna, sun kashe dan bindiga 1

A wani labarin, wata tawagar hadin gwiwa ta yan sanda da sojoji sun yi nasarar dakile wani hari da aka yi yunkurin kaiwa kan kauyen Akwando da ke karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna a ranar Litinin.

Kakakin yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige ya bayyana a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, cewa dakarun sun halaka daya daga cikin maharan sannan suka kwato bindigar AK47 guda daya, Premium Times ta rahoto.

Mista Jalige ya yi bayanin cewa tawagar ta yi aiki ne bayan ta samu rahoto da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Litinin cewa wasu da ake zaton yan bindiga ne sun farmaki kauyen Akwando.

Kara karanta wannan

Ashe makiyaya ne ba ‘Yan bindiga ba – ‘Yan Sanda sun yi karin haske kan bidiyon da ke yawo

Asali: Legit.ng

Online view pixel