Batun rashin tsaro: Tsohon ministan Buhari ya yiwa shugaban kasar wankin babban bargo

Batun rashin tsaro: Tsohon ministan Buhari ya yiwa shugaban kasar wankin babban bargo

  • Barista Solomon Dalung, tsohon ministan matasa da wasanni, ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda matsalar rashin tsaro
  • Dalung ya ce tsohon ubangidan nasa ya gaza cika alkawaran da ya daukarwa yan Najeriya na kare rayuka da dukiyoyinsu
  • Tsohon ministan ya kuma bayyana cewa Buhari ya basu kunya saboda duk da kasancewarsa Janar gashi suna raba iko da Bello Turji wanda ya addabi arewa maso yamma

Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gazawa yan Najeriya sannan cewa ya baiwa mutane da dama kunya ciki harda shi saboda ya kasa magance matsalar rashin tsaro a kasar.

Dalung ya bayyana hakan ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 10 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Zan daura daga inda Buhari ya tsaya: Alkawura 10 na Osinbajo idan ya zama shugaba a 2023

Tsohon ministan ya kuma koka kan cewa shugaban kasar na raba iko tare da kasurgumin shugaban yan bindiga na arewa maso yamma, Bello Turji da kuma mayakan ISWAP sakamakon gazawarsa wajen magance rashin tsaro.

Batun rashin tsaro: Tsohon ministan Buhari ya yiwa shugaban kasar wankin babban bargo
Batun rashin tsaro: Tsohon ministan Buhari ya yiwa shugaban kasar wankin babban bargo Hoto: Barrister Solomon Dalung, Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Har ila yau, Dalung ya bayyana cewa ya shiga sahun sauran yan Najeriya wajen yiwa APC da shugaba Buhari kamfen saboda rashin jin dadin yadda gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ke tafiyar da matsalar tsaro a kasar a wancan lokacin.

Ya bayyana cewa ya gana da tsohon shugaban kasar sannan ya bashi shawara kan yadda zai magance hauhawan rashin tsaro a lokacin, amma aka yi watsi da shawararsa.

Ya ce:

“A karkashin Goodluck Jonathan an yi ta kashe mutane a Filato, ana tayar da wuraren bauta, ofishoshin gwamnati da kamfanoni da bama-bamai, ana ta kashe-kashe, fille kawuna da sace mata da yaran makaranta a arewa maso gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Karka damu: Shugaba Buhari ya jajantawa tsohon shugaba Jonathan game da mutuwar mukarrabansa

“Martanin da gwamnatin Jonathan ta bayar kan wannan ta’asa ba na hankali bane kuma sau da yawa ba wanda ya dace ba kamar yadda ake tsammani daga gwamnati.
“Na jagoranci tafiyar “Chanji” kan gwamnatin bayan ganawa da Shugaba Jonathan sau da dama tare da bashi shawara kan mafita wanda ba wai an yi watsi bane da shi kawai illa an dauke ni a matsayin makiyin kasa tare da kokarin daukar rayuwata.”

Sai dai Dalung, wanda ya yi ikirarin cewa ya zama abun ki a al’umman kirista saboda shiga kamfen din adawa da gwamnatin Jonathan ya ce koda dai Buhari ya samu wasu nasarori a bangaren samar da ababen rayuwa, amma ya kasa cika alkawarinsa na kare rayuka da dukiyar yan Najeriya, daya daga cikin muhimman tsare-tsaren da suka sa aka zabe shi.

Ya kara da cewa:

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari dan Najeriya ne mai nufin kasar da alkhairi kuma yana da rikon amana, ina son shi sosai amma rikon amana kadai bai isaba a wannan yanayi, magana ta gaskiya, Baba Buhari ya gazawa yan Najeriya kuma y aba mutane da yawa kunya ciki harda ni.

Kara karanta wannan

Buhari ya gaza, kuma bai shirya magance matsalar rashin tsaro ba, inji Sanata mai ci

“Shugaba Buhari ya yi kokari wajen samar da ababen more rayuwa, amma a karkashin kulawarsa ‘yan fashi da masu ta’addanci na ci gaba da bunkasa ba tare da wani hukunci ba, kuma shi din Janar ne, tsohon shugaban kasa a mulkin soja kuma kwamandan rundunar soji. Me yasa shugaban kasa zai raba mulki tare da Bello Turji da ISWAP?
"Dole ne ka saurari muryar hankali, a gyara tsarin tsaro, a murkushe yan ta’adda kafin ka bar mulki idan ba haka ba mu magoya bayan ka ba za mu samu damar kare mutuncin ka ba" Wannan ita ce shawarata ta karshe ga Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 3 ga Maris 2020. Ban sake samun damar tattaunawa da shi ba tun daga lokacin duk da shan neman yin hakan.
“Ba zan yi kasa a gwiwa ba wajen magana kan rashin adalci da rashin tsaro ba saboda “idan har yanzu ina neman burge mutane, toh ban cancanci zama dan aiken almasihu ba.”

Kara karanta wannan

Za a Iya Kawo Karshen 'Yan Ta'adda Cikin Watanni 6, Shugabannin Tsaro Masu Murabus

Matsalolin da Najeriya ke fuskanta alamun daukaka ne, In ji dan majalisa daga arewa

A wani labarin, dan majalisar dokokin tarayya daga jihar Sokoto, Ibrahim Almustapha, ya bayyana cewa matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu alamu ne na daukaka, cewa kasar na da ikon za ta iya tsallake su.

Almustapha wanda ke wakiltan mazabar Wurno/Rabah na jihar Sokoto a majalisar wakilai, ya bayyana hakan ne da yake zantawa da manema labarai a garin Sokoto a ranar Lahadi, Premium Times ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng