Buhari ya gaza, kuma bai shirya magance matsalar rashin tsaro ba, inji Sanata mai ci

Buhari ya gaza, kuma bai shirya magance matsalar rashin tsaro ba, inji Sanata mai ci

  • Sanata mai ci ya caccaki gwamnatin Buhari, inda yace sam shugaba Buhari bai shirya magance matsalar tsaro ba
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a jiharsa ta Edo , inji rahoton jaridar Punch
  • Hakazalika, ya yi tsokaci kan yadda majalisar dokokin kasar ta yi kokari wajen ganin an magance matsalolin kasar nan

Benin, Edo - Sanata mai wakiltar mazabar Edo ta Kudu a majalisar dattawa, Sanata Matthew Urhoghide, a ranar Laraba ya ce shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya nuna gazawa matuka wajen magance matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Sanatan wanda ya wakilci mazabarsa a majalisar dattijai ta 8 da ta 9, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Benin na jihar Edo.

Kara karanta wannan

An kai makura: Gwamnoni da shugabannin majalisa za su gana don tattauna batun tsaro

Sanata ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari kan lamarin tsaron kasar nan
Buhari ya gaza, bai shirya magance matsalar rashin tsaro ba – Sanata | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Ya ce:

“Bari in ce duk wani dan Najeriya ya damu matuka game da matsalar tsaro a kasar nan, kuma abubuwan da suka faru a makwannin da suka gabata sun nuna cewa Gwamnatin Tarayya ba ta shirya magance matsalar rashin tsaro a kasar nan ba."

Ya kuma bayyana cewa, majalisar dokokin kasar nan ta yi aikinta yadda ya kamata, inda yace ta yi kokari wajen amincewa da kudurin daukar ma'aikatan tsaro, sayen makamai da dai sauran abubuwan magance matsalar tsaro.

Ya koka kan shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa:

“Shugaban kasa ya nuna gazawa da yawa kuma da yawa daga cikinmu sun yi imanin cewa ba ya son yin komai, in ba haka ba, babu dalilin da zai sa mu shiga cikin wannan mawuyacin hali, inda kowa a Najeriya a yau bai da tabbacin zai rayu a minti na gaba.

Kara karanta wannan

ASUU ga FG: Ba zai yiwu ku yaki rashin tsaro ba yayin da kuka mayar dalibai 'yan zaman kashe wando

Ya kuma koka kan yadda hanyar Abuja zuwa Kaduna ta saka taskar mutuwa ga 'yan Najeriya, inda yace:

"Idan wani na son kashe kansa a Najeriya, hanya mafi sauki ta yin haka ita ce ta bin hanyar mota daga Abuja zuwa Kaduna, domin mutum yana da 50% na tabbacin rashin dawowa kuma gwamnatin tarayya ta san hakan."

Jami'an tsaro sun yi kadan a Najeriya

Ya ce karancin ma’aikata a cikin sojoji da na ‘yan sanda ya sa ba su iya wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

A cewarsa:

“Akwai matukar karancin ma’aikata a cikin sojoji da kuma sauran jami’an tsaro. Muna da kididdigar da za mu nuna cewa duk jami’an tsaro da ake dasu (Sojoji, Sojojin Sama, Na ruwa, har da Kwastam) ba su kai miliyan 1.2 ba a kasa mai mutane miliyan 200.

Ya kuma bayyana cewa, majalisa ta nemi hukumar 'yan sanda ta daukar ma'aikata da akalla 10,000 duk shekara, amma har yanzu abin ya ci tura, inji rahoton Daily Sun.

Kara karanta wannan

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

Ya kuma kara da cewa:

"Ina so in gaya muku cewa tun shekaru hudu da aka yanke wannan batu, 'yan sandan Najeriya ba su dauki wannan adadin ba."

Wadanda suka kai hari jirgin Abuja-Kaduna sun saki bidiyo, sun ce ba kudi suke bukata ba

A wani labarin, 'yan ta'addan da suka kai hari jirgin kasan Abuja-Kaduna sama da mako daya sun saki bidiyonsu na farko tun bayan harin da yayi sanadiyar halakar mutum akalla takwas.

A sabon bidiyon da suka saki ranar Laraba, sun bayyana cewa ba kudi suke bukata ba, gwamnati ta san abinda suke bukata.

Sun haska bidiyon ne tare da Shugaban bankin noma, Alwan Hassan, inda suka ce zasu sake shi albarkacin tsufarsa da watar Ramadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel