Karka damu: Shugaba Buhari ya jajantawa tsohon shugaba Jonathan game da mutuwar mukarrabansa

Karka damu: Shugaba Buhari ya jajantawa tsohon shugaba Jonathan game da mutuwar mukarrabansa

  • Shugaba Buhari Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga tsohon shugaba Jonathan na Najeriya bisa mutuwar mukarrabansa
  • A makon nan ne aka samu labarin mutuwar mukarraban Jonathan guda biyu a hadarin mota a babban birnin tarayya Abuja
  • Buhari ya bi sahu, ya shiga jerin 'yan Najeriyan da suka nuna alhini bisa wannan rashi mai matukar ban takaici

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa tsohon shugaban Najeriya; Good Ebele Jonathan bisa rashin wasu mukarabbansa biyu a hadarin mota.

Idan baku manta ba, a cikin makon nan ne rahotanni suka karade kafafen watsa labaran Najeriya, inda aka bayyana yadda hadarin mota ya rutsa da tawagar tsohon shugaban kasar a Abuja.

Buhari ya yi jajan mutuwar mutane biyu na Jonatha
Karka damu: Shugaba Buhari ya jajantawa tsohon shugaba Jonathan game da hadarin mota | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jim kadan bayan faruwar hadarin, jiga-jigan 'yan Najeriya daga sassa daban-daban na kasar suka fara aiko da sako jaje da nuna alhini ga Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan

Haɗarin Mota: Za Mu Nakasa Tattalin Arzikin Najeriya Idan Wani Abu Ya Faru Da Jonathan, Matasan Neja Delta

Shugaba Buhari, ya bi sahunsu, inda ya fitar da sakon jaje ta hannun mai magana da yawunsa; Mallam Garba Shehu a yau Juma'a 8 ga watan Afirilu.

Sanarwar da Garba Shehu ya yada a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa:

"Shugaba Muhammadu Buhari ya jajantawa tsohon shugaban kasa Goodluck Ebebe Jonathan bisa mutuwar wasu ma'aikatansa guda biyu a hadarin mota."

A bangare guda, shugaban ya kuma bayyana godiyar ga Allah bisa tseratar da Jonathan daga hadarin ba tare da wani rauni ba, inda ya nemi tsohon shugaban kasar da kada ya karaya da gudanar da tafiye-tafiyensa na ciki da wajen kasa.

Ya auna arziki: Mummunan hadari ya rutsa da tsohon shugaban kasa Jonathan

A wani labarin, a yammacin yau Laraba ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi hatsarin mota a Abuja wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mukarrabansa biyu, inji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan: Yadda ‘Yan Sandan da ke kula da ni, suka mutu nan-take a hadarin mota

Daya daga cikin masu taimaka masa, wanda ya tabbatar da afkuwar hatsarin, ya ce Jonathan na cikin koshin lafiya.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, an ce tsohon shugaban yana gida. Hadarin ya afku ne a lokacin da tsohon shugaban kasan ke kan hanyar sa daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe zuwa gidansa da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel