Zan daura daga inda Buhari ya tsaya: Alkawura 10 na Osinbajo idan ya zama shugaba a 2023

Zan daura daga inda Buhari ya tsaya: Alkawura 10 na Osinbajo idan ya zama shugaba a 2023

Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa, ya bayyana abubuwan da yake so ya yiwa 'yan Najeriya matukar suka bashi dama ya dane kujerar Buhari a zaben 2023 mai zuwa

Bayan taron liyafar buda baki da gwamnonin jam'iyyar APC a jiya Lahadi, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, TheCable ta ruwaito.

Yayin da yake jawabin ne ya bayyana irin alkawuran da ya yiwa 'yan Najeriya, inda ya ce zai daura daga inda shugaba Buhari zai tsaya a karshen mulkinsa.

Kudurorin Osinbajo gabanin zaben 2023 yayin da ya ayyana kudurin gaje Buhari
Zan daura daga inda Buhari ya tsaya: Alkawuran Osinbajo idan ya zama shugaba a 2023 | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Twitter

Mataimakin shugaban kasar ya ce shirinsa shi ne kafa "Najeriya ta mafarkin mu a cikin 'yan shekaru kadan".

Alkawura 10 da Osinbajo ya yiwa 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Shugaban kasa: Yadda Farfesa Yemi Osinbajo zai ayyana shirin gaje kujerar Buhari a yau

A jawabinsa, Osinbajo ya bayyana abubuwan da yake son cimmawa idan ya gaji Buhari a zaben 2023 mai zuwa, inda ya ce ya sanya abubuwa kamar haka a gabansa, kamar yadda jaridar Punch ta tattaro:

  1. Samar da kyakkyawan yanayi don bunkasa harkar kasuwanci
  2. Daukaka harkar noma zuwa mataki na gaba musamman wajen amfani da injuna da inganta aikin gona zuwa abu mafi kima
  3. Tabbatar da cewa gwamnati da hukumominta da masu kula da harkokinta sun yi wa ‘yan kasuwa hidima
  4. Samar da tattalin arzikin fasaha wanda zai samar da ayyukan yi ga miliyoyi
  5. Habaka Shirin Zuba Hannun Jari na Jama'a zuwa cikakken tsarin jin dadin rayuwar jama'a
  6. Kammala alkawarin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin wadannan shekaru goma
  7. Kammala aikin tabbatar da cewa dukkan 'yan Najeriya maza da mata suna halartar makaranta
  8. Gyara tsarin karatun mu ya dace da kalubalen wannan karni na 21
  9. Kammala aikin bayar da tallafin kiwon lafiya ga kowa da kowa
  10. Da kuma karfafa karfin Jihohi da Kananan Hukumomi wajen gudanar da ayyukansu yadda ya dace

Kara karanta wannan

Yan Najeriya zasu zabi APC a 2023 saboda gwamnati na ta yi namijin kokari, Shugaba Buhari

Mataimakin shugaban ƙasa ya ayyana aniyar gaje Buhari a 2023

A wani labarin, daga karshe dai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ayyana nufinsa na neman takarar shugaban kasa a babban zaben 2023 dake tafe.

Mataimakin shugaban ya ayyana aniyarsa a hukumance ne a wani gajeren Bidiyo da ya saka a shafinsa na Twitter bayan shafe watanni ana rade-radi.

Osinbajo ya ce:

"Ni a yau, tare da matukar kankan da kai ina mai ayyana nufina na neman ofishin shugaban kasan tarayyar Najeriya a hukumance karkashin inuwar jam'iyyar All Progressive Congress (APC)."

Asali: Legit.ng

Online view pixel