Yanzu-Yanzu: Buhari ya yi sabon nadi, ya nada sabon ministan muhalli

Yanzu-Yanzu: Buhari ya yi sabon nadi, ya nada sabon ministan muhalli

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi umurnin mayar da Mohammed Abdullahi ma’aikatar muhalli a matsayin sabon minista
  • Kafin nadin nasa, Abdullahi ya kasance karamin ministan kimiyya da fasaha
  • Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, wanda ya sanar da nadin a ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu, ya ce nadin ya fara aiki nan take

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mohammed Abdullahi a matsayin ministan muhalli.

Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ne ya sanar da nadin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu, jaridar The Cable ta rahoto.

Yanzu-Yanzu: Buhari ya yi sabon nadi, ya nada sabon ministan muhalli
Yanzu-Yanzu: Buhari ya yi sabon nadi, ya nada sabon ministan muhalli Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Sanarwar ta kuma bayyana cewa nadin ya fara aiki nan take.

Kafin mayar da shi ma’aikatar muhalli domin yin jagoranci, Abdullahi, ya kasance karamin ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ya auna arziki: Mummunan hadari ya rutsa da tsohon shugaban kasa Jonathan

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce:

“Shugaban kasa na fatan cewa zai kawo tarin kwarewarsa a sabon aikinsa domin ci gaban kasar.”

An yi a banza: An kashe N1.3trn amma wutar lantarki bata gyaru ba, ministar kudi

A wani labarin, ministar kasafin kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta ce kudade Naira tiriliyan 1.3 da gwamnatin tarayya ta tanadar a bangaren samar da wutar lantarki basu haifar da da mai ido ba, inji rahoton TheCable.

A ranar 1 ga Maris, 2017, FG ta amince da kashe N701bn domin inganta wutar lantarki ga Kamfanin Dillalan Wutar Lantarki ta Najeriya (NBET) domin biyan kudin da GenCos ke samarwa ga ma’aikatar wuta ta kasa na tsawon shekaru biyu.

An bayar kudaden ne domin tunkarar kalubalen kudi na wata-wata da GenCos ke fuskanta, yayin da kamfanonin rarraba wuta (DisCos) ke ci gaba da gazawa wajen biyan kudaden wutar lantarkin da ake rarrabawa duk wata.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya rattafa hannu kan sabuwar dokar wajabta kula da ofishoshin gwamnati

Asali: Legit.ng

Online view pixel