Shugaba Buhari ya rattafa hannu kan sabuwar dokar wajabta kula da ofishoshin gwamnati

Shugaba Buhari ya rattafa hannu kan sabuwar dokar wajabta kula da ofishoshin gwamnati

  • Shugaba Buhari ya kafa sabuwar dokar wajabta kula da dukiya da ofishohin gwamnatin tarayya
  • Shugaban kasa ya ce wannan dokar zata wajabtawa ma'aikatu kafa sashe na musamman don haka
  • Buhari ya jagoranci zaman majalisar FEC na yau ta yanar gizo

Aso VIlla, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan sabuwar umurni ta 11 dake wajabta kula da ofishohin gwamnati yadda ya kamata.

Buhari ya rattafa hannu kan sabuwar dokar ne gabanin taron majalisar zartaswa na ranar Laraba, 6 ga watan Maris, 2022.

Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya bayyana hakan.

Shugaba Buhari
Da duminsa: Shugaba Buhari ya kafa sabuwar dokar wajabta kula da ofishoshin gwamnati Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Shugaban kasan ya umurci ma'aikatu da hukumomin gwamnati su kafa sabon sashen kula da ofishohi kamar yadda sabuwar dokar ta bukata.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta baiwa matasa guda 98,000 bashin kudin N50,000 zuwa N300,000: Sadiya

Ya ce kula da dukiyar gwamnati zai bada guraben aiki ga matasan Najeriya.

Gwamnati za ta baiwa matasa guda 98,000 bashin kudin N50,000 zuwa N300,000: Sadiya

A wani labarin kuwa, Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kammala shirin baiwa yan Najeriya mutum 98,000 bashi maras kudin ruwa cikin tsarin Government Enterprise and Empowerment Programme (GEEP) 2.0.

Ministar walwala, tallafi da jin dadin mutane, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana hakan a jawabin da mai magana da yawunta, Nneka Anibeze, ta fitar ranar Laraba, rahoton NAN.

Hajiya Sadiya ta ce wadanda aka zaba zasu samu bashin kudi N50,000 zuwa N300,000.

Tace wadanda aka zaba zasu samu sakon taya murna nan ba da dadewa ba.

Ta kara da cewa duk wanda aka baiwa kudin ya san ba kyauta aka bashi ba, bashi ne kuma zai biya nan da watanni tara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel