Ya auna arziki: Mummunan hadari ya rutsa da tsohon shugaban kasa Jonathan

Ya auna arziki: Mummunan hadari ya rutsa da tsohon shugaban kasa Jonathan

  • An samu aukuwar hatsarin mota da ya rutsa da ayarin motocin tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, a Abuja a ranar Laraba, 6 ga Afrilu
  • An ce tsohon shugaban kasar yana cikin koshin lafiya, amma rahotanni sun nuna cewa wasu mukarrabansa biyu ana fargabar sun mutu a hatsarin
  • An ce Jonathan na kan hanyarsa ne daga filin jirgin saman Nnamdi Azikwe zuwa gidansa da ke Abuja a lokacin da hatsarin ya afku

A yammacin yau Laraba ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi hatsarin mota a Abuja wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mukarrabansa biyu, inji rahoton Leadership.

Daya daga cikin masu taimaka masa, wanda ya tabbatar da afkuwar hatsarin, ya ce Jonathan na cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari Masallaci lokacin bude baki, sun kashe mutum 3, sun yi awon gaba da wasu

Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaban kasa Jonathan ya auna arziki, motarsa ta yi hatsari
Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaban kasa Jonathan ya auna arziki, motarsa ta yi hatsari
Asali: Original

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, an ce tsohon shugaban yana gida.

Hadarin ya afku ne a lokacin da tsohon shugaban kasan ke kan hanyar sa daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe zuwa gidansa da ke Abuja.

Sai dai, jaridar TheCable ba ta ba da rahoton mutuwar mutane a hadarin ba. Jaridar ta bayyana cewa ana fargabar mutane biyu sun mutu a hadarin, amma har yanzu ba a tantance ko su wane ne wadanda suka mutu ba.

A cewar majiyoyi daga makusanta Jonathan, har yanzu tsohon shugaban kasar yana Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, har zuwa safiyar Laraba.

An ce ya tafi Abuja ne domin wani aiki a hukumance.

Hukumar FRSC ta tabbatar da afkuwar hatsarin, ta yi karin haske

Jaridar Leadership a wani sabon rahoto da ta fitar ta ce hukumar FRSC ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a hatsarin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya rattafa hannu kan sabuwar dokar wajabta kula da ofishoshin gwamnati

Kakakin hukumar FRSC, Bisi Kazeem, ya ruwaito cewa wasu mataimaka guda biyu kuma suna kwance a asibitin kasa dake Abuja bayan da suka samu munanan raunuka daban-daban.

Hukumar FRSC ta kuma ce tsohon shugaban bai samu rauni ba saboda motar da yake ciki ba ta cikin wadanda suka yi hatsarin.

Wadanda suka kai hari jirgin Abuja-Kaduna sun saki bidiyo, sun ce ba kudi suke bukata ba

A wani labarin, yan ta'addan da suka kai hari jirgin kasan Abuja-Kaduna sama da mako daya sun saki bidiyonsu na farko tun bayan harin da yayi sanadiyar halakar mutum akalla takwas.

A sabon bidiyon da suka saki ranar Laraba, sun bayyana cewa ba kudi suke bukata ba, gwamnati ta san abinda suke bukata.

Sun haska bidiyon ne tare da Shugaban bankin noma, Alwan Hassan, inda suka ce zasu sake shi albarkacin tsufarsa da watar Ramadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel