Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

  • Jami'an hukumar DSS sun yi nasarar kame wasu mutane da ake zargi da hada tawagar sace yara kanana
  • Daga cikin wadanda aka kama, an samu mata da miji, inda aka ce matar mai shayarwa ita ke adana musu makamai
  • Gwamnatin jihar Ondo ta yi tsokaci kan wannan lamari, inda tace aikin tsaro aiki ne na kowa, ya kamata 'yan jihar su taimaka da bayanai

Jihar Ondo - Hukumar ‘yan sandan farin kaya (DSS) ta kama wasu mutane shida ciki har da wata mata mai shayarwa, gogaggu wajen sace 'ya'yan jama'a kanana a jihar Ondo.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a jiya ne aka gabatar da wadanda ake zargin a ofishin DSS da ke Akure, babban birnin jihar.

Daraktan DSS a jihar, Mista Jonathan Kure, ya bayyana cewa mutanen da aka kaman tuni dama sun addabi jihar ta hanyar sace kananan yara ‘yan shekara biyu zuwa hudu.

Kara karanta wannan

Dankwambo ya dawo Gombe bayan shekaru 3, ya ce har yanzu PDP ce burin talaka

DSS ta kame mutum 6 da ake zargi da sace yaro dan shekara 2
Yadda DSS suka kama wasu da suka shahara wajen sace kananan yara a Ondo | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya ce an yi nasarar zakulowa tare da kamo su ne biyo bayan wani rahoto na sirri da aka samu kan munanan ayyukansu a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa an gudanar da aikin ne cikin hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro musamman rundunar sojin Najeriya.

A cewarsa, uwar mai shayarwa, wadda matar daya daga cikin wadanda aka kaman ne takan taimaka wajen ajiye makamai.

Kure ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala cikakken bincike, inji rahoton Punch.

Abin takaici, har da uwa mai shayarwa cikin masu laiifin

A cewarsa:

“Abin da ya fi jan hankali ma shi ne cewa daya daga cikin mambobinsu uwa ce mai shayarwa kuma matar daya daga cikin masu garkuwa da mutanen. Har ila yau, tana taka rawa biyu na kasancewa ma'ajiyar makaman tawagar."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Amaechi Ya Shiga Jerin Masu Son Ɗare Wa Kujerar Buhari a 2023

Ya ce abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da na’urorin tafi da gidanka, kudi da kuma bindigogi kirar gida.

Mataimakin gwamnan jihar, Mista Lucky Aiyedatiwa, ya baiwa mazauna jihar tabbacin samun isasshen tsaro da kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Aiyedatiwa ya bukaci masu ba da gidajen haya da su nemi bayanan wadanda za su ba haya yadda ya kamata kuma su san irin aikin da suke yi.

A cewarsa:

“Tsaro aikin kowa ne. Idan kun lura da wanda ke rayuwa fiye da yadda ya kamata, ya kamata jami'an tsaro su binciki mutumin."

Wadanda suka sace basaraken Abuja sun nemi iyalansa su siyar da gidansa don hada masu miliyan N20 kudin fansa

A wani labarin, wadanda suka yi garkuwa da basaraken garin Bukpe da ke yankin Kwali ta birnin tarayya sun umurci iyalansa da su siyar da gidansa domin hada naira miliyan 20 da suka bukata na fansarsa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, sun kashe 9 a jihar Neja

Daily Trust ta rahoto yadda masu garkuwa da mutane suka farmaki fadar basaraken, Mai Martaba Alhaji Hassan Shamidozhi, a daren ranar Laraba.

Jaridar ta kuma rahoto cewa a lokacin da ta ziyarci garin a ranar Lahadi, wani ahlin gidan basaraken, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce masu garkuwa da mutanen sun sha alwashin cewa ba za su sake shi ba har sai sun samu naira miliyan 20.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel