An kai makura: Gwamnoni da shugabannin majalisa za su gana don tattauna batun tsaro

An kai makura: Gwamnoni da shugabannin majalisa za su gana don tattauna batun tsaro

  • Gwamnonin Najeriya 36 za su yi ganawar gaggawa domin dinke matsalolin da suka addabi kasar nan
  • Hakazalika, a ganawar tasu, shugabannin majalisu daga jihohi za su halarta, duk dai domin nemo mafita ga Najeriya
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kasar ke kara fuskantar matsalolin cikin gida, ciki har da tsaro

FCT, Abuja - Dangane da matsalar tsaro da ake fama da ita a fadin kasar nan, gwamnonin jihohi 36 da shugabannin majalisar dokokin kasar za su yi wani taron gaggawa ranar Juma’a mai zuwa a Abuja, inji rahoton Daily Trust.

Taron dai za a yi shi ne don tattauna matsalolin rashin tsaro da sauran batutuwan da suka shafi kasa baki daya.

Gwamnoni da shugabannin majalisu za sau yi ganawar gaggawa
An kai makura: Gwamnoni da shugabannin majalisa za su gana don tattauna batun tsaro | Hoto: allnigeriainfo.ng
Asali: Depositphotos

Shugaban yada labarai da hulda da jama’a a kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), Mista Abdulrazak Bello-Barkindo, ya bayyana a ranar Talata a Abuja cewa mahalarta taron za su yi tunani don nemo hanyoyin magance matsalolin da ke addabar kasar.

Kara karanta wannan

2023: Tambuwal da Peter Obi za su shiga labule da masu ruwa da tsaki na PDP a majalisar tarayya a yau

Bello-Barkindo ya nakalto Darakta-Janar na NGF, Mista Asishana Okauru, yana cewa:

"Ana sa ran amincewar Majalisar Zartaswa da Majalisar Dokoki za ta mamaye zukatan mutane 72 da za su halarta."

Daily Sun ta tattaro cewa, ya kuma ambato Okauru na cewa:

“Taron za a yi shi ne don cimma matsaya cikin gaggawa domin kuwa za a gabatar da muhimman batutuwa kamar tsaron rayuka da dukiyoyi a Najeriya baki daya’’.

Sanarwar ta kara da cewa shugaban NGF, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya gargadi gwamnonin da su gaggauta tare da baiwa shugabannin majalisun jihohinsu damar halarta.

Gwamnatin Zamfara ta yi gargadi game da watsa lambobin wayar Matawalle a soshiyal midiya

A wani labarin, Gwamnatin Zamfara ta gargadi mazauna jihar kan amfani da lambar wayar Gwamna Bello Matawalle ba tare da izini ba, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

Gargadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai ba gwamnan shawara ta musamman kan wayar da kan jama’a, Mista Zailani Bappa, a ranar Talata, 5 ga watan Afrilu.

Sanarwar ta ce: “Manufar mai girma gwamna na barin lambobin wayarsa su fita cikin al’umma shine domin saka idanu sosai kan lamuran tsaro da kuma lamuran ci gaba daga tushe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel