Gwamnatin Zamfara ta yi gargadi game da watsa lambobin wayar Matawalle a soshiyal midiya

Gwamnatin Zamfara ta yi gargadi game da watsa lambobin wayar Matawalle a soshiyal midiya

  • Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya gargadi al'umman jihar kan amfani da lambar wayarsa ba bisa ka'ida ba
  • Matawalle dai ya ce bayan sakin lambarsa da manufar magance matsalar rashin tsaro a jihar sai wasu suka fara saka shi a shafukan soshiyal midiya marasa amfani
  • Gwamnatin jihar ta ce duk wanda ke da burin amfani da lambar gwamnan a shafi na soshiyal midiya toh ya nemi izini daga ofishin hadiminsa

Zamfara - Gwamnatin Zamfara ta gargadi mazauna jihar kan amfani da lambar wayar Gwamna Bello Matawalle ba tare da izini ba, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Gargadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai ba gwamnan shawara ta musamman kan wayar da kan jama’a, Mista Zailani Bappa, a ranar Talata, 5 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

An kai makura: Gwamnoni da shugabannin majalisa za su gana don tattauna batun tsaro

Gwamnatin Zamfara ta yi gargadi game da watsa lambobin wayar Matawalle a soshiyal midiya ba tare da izini ba
Gwamnatin Zamfara ta yi gargadi game da watsa lambobin wayar Matawalle a soshiyal midiya ba tare da izini ba Hoto: bbc.com
Asali: Facebook

Sanarwar ta ce:

“Manufar mai girma gwamna na barin lambobin wayarsa su fita cikin al’umma shine domin saka idanu sosai kan lamuran tsaro da kuma lamuran ci gaba daga tushe.
“Ya kuma mayar da shi dabi’a don saka idanu a shafukan soshiyal midiya don jin doriyar mutane da kansa.
“Ya yi hakan ne don ci gaba da bayar da fifiko ga muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sanya a gaba kamar yadda mutane ke muradi.
“Sai dai kuma, wasu mutane masu sakaci suna wofantar da wannan damar ta hanyar saka lambar mai girma gwamna a shafukan soshiyal midiya marasa amfani ba tare da izini ba.”

Ya kuma shawarci jama’a da ke burin saka lambar gwamnan a kowani dandamali na soshiyal midiya da su nemi izini daga ofishin mai bashi shawara na musamman kan wayar da kan jama’a, labarai da sadarwa, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Dankwambo ya dawo Gombe bayan shekaru 3, ya ce har yanzu PDP ce burin talaka

Matsalar tsaro ta fatattaki Bayin Allah 700, 000 daga gidajensu a Zamfara inji Kwamishina

A wani labarin, gwamnatin jihar Zamfara ta ce ma’aikatar bada agaji ta kafa cibiyoyi takwas domin kula da wadanda su ke sansanin gudun hijira a garuruwan jihar.

Daily Trust ta rahoto gwamnatin ta na cewa akwai sama da mutane 700, 000 da ke gudun hijira.

Kwamishinan yada labarai na Zamfara, Ibrahim Magaji Dosara ya shaidawa manema labarai a Kaduna cewa gwamnati na dawainiya da masu gudun hijira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel