Damfara: An kama 'yar shekara 24 da ta addabi Kanawa da sata da katunan ATM

Damfara: An kama 'yar shekara 24 da ta addabi Kanawa da sata da katunan ATM

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce an gurfanar da wacce ake zargi, Osasi Chinozom Juliet a gaban kotu domin yi mata shari’a
  • Juliet ta yi ikirari cewa ta sace katunan ATM da yawa daga bankuna daban-daban tare da cire kudaden jama'a
  • An tattaro cewa Juliet na cikin jerin sunayen wadanda ‘yan sanda ke nema kafin jami’an sintiri na ‘yan sandan Kano su kama ta

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wata budurwa ‘yar shekara 24 mai suna Osasi Chinozom Juliet bisa laifin damfarar mutane ta katunan ATM din su, inji rahoton DailyTrust.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa an kwato fiye da katunan ATM guda 15 daga hannun Juliet da ake zargi.

Yadda aka kama 'yan damfara
Damfara: An kama 'yar shekara 24 da ta addabi Kanawa da sata ta ATM | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Legit.ng ta kuma tattaro cewa Juliet ta kasance cikin jerin sunayen wadanda hukumar 'yan sandan jihar Kano ke nema kafin a kama ta.

An ce Juliet ta kware wajen damfarar mutane da katin ciran kudi a wuraren cire na ATM da ke cikin babban birnin Kano.

Da take bayani, Juliet ta bayyana cewa tana da dukkan katunan cire kudi na dukkan bankunan da ta ke yiwa jama'a sata.

Ta ci gaba da bayyana cewa ta sha kare kudi a lokuta da dama a duk lokacin da ta yi nasarar satar katin cire kudin wadanda ta damfara, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Yadda 'yan sanda suka kama Juliet

A bangare guda, an tattaro cewa an samu nasarar cafke ta ne bayan da jami’an tsaron sintiri suka kama ta a kan hanyar Enugu a Sabon Gari.

Kiyawa ya ce:

“Bayan kama ta, wani Yusuf Tijjani, ‘mnamiji, ya koka da cewa, a ranar 17/03/2022, wacce ake zargin ta neme shi a lokacin da take neman taimakonsa a na’urar ATM, cikin yaudara, ta canza masa katin ATM, sannan ta cire kudi N15,000:00 daga asusunsa."

Rundunar ‘yan sandan Kano ta ce za a gurfanar da wacce ake zargin a gaban kotu fuskantar shari'a.

Gabansa ba ya aiki: Tsohuwa mai shekaru 54 ta nemi saki a gaban kotu

A wani labarin, wata mata ‘yar shekara 54 mai suna Blessing Mormah ta garzaya wata kotun al’adu ta Igando inda ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda ganin cewa mijin ba a iya gamsar da ita wajen jima’i.

Matar mai sana'ar kwalliya mai suna Mormah ta roki kotu a ranar Talata da ta raba aurenta da ya shafe shekara 25 tana mai ikrarin cewa, dama an tilasta mata yin auren ne, The Nation ta ruwaito.

Hakazalika, ta bayyana yadda take dama dashi duk lokacin da rikici ya barke a tsakaninsu, inda tace korarta yake daga gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel