Kaduna: 'Yan bindiga sun kai mugun farmaki sansanin soji, sun sheke dakaru 11

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai mugun farmaki sansanin soji, sun sheke dakaru 11

  • An rasa rayukan sojoji 11 inda wasu 19 suka jigata a mummunan harin da 'yan bindiga suka kai sansanin sojoji a Birnin Gwari
  • Majiya mai tushe daga cikin sojojin ta ce miyagun sun bayyana da yawansu dauke da makamai inda aka yi musayar wuta kafin su tsere
  • Tuni aka garzaya da sojojin da suka jigata asibitin Birnin Gwari yayin da aka kwashe gawawwakin mamatan zuwa asibitin 44 na Kaduna

Birnin Gwari, Kaduna - A kalla sojoji 11 ne aka kashe a mugun hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a wani sansanin soji da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, kamar yadda majiya ta shaida wa TheCable.

‘Yan bindigar da suka isa sansanin da yawansu sun kutsa cikin sansanin da ke kauyen Polwire a ranar Litinin da ta gabata inda suka yi artabu da sojojin.

Kara karanta wannan

Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC

Majiyar soji ta shaida wa jaridar TheCable cewa, ‘yan bindigar sun bayyana a kan babura kuma suna dauke da manyan makamai da suka hada da gurneti (RPG).

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai mugun farmaki sansanin soji, sun sheke dakaru 30
Kaduna: 'Yan bindiga sun kai mugun farmaki sansanin soji, sun sheke dakaru 30. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

An sanar da cewa an dauki kimanin sa'o'i biyu ana gwabza fada kafin a fatattaki 'yan ta'addan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mun yi asarar sojoji 11 yayin da sojoji 19 suka samu miyagun raunuka, bayan da 'yan ta'addan suka far wa sojojin. Hakazalika sun kona motocin yaki masu sulke (APC) guda uku,” in ji wata majiya daga sojojin.

An gano cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da makamai da dama na sojojin.

TheCable ta gano cewa, an kwashe sojojin da suka jigata zuwa babban asibitin Birnin Gwari da kuma cibiyar kula da lafiya ta sojojin saman Najeriya 271.

An kwashe wadanda aka kashe zuwa Asibitin Reference na Sojojin Najeriya 44 Kaduna (44 NARHK) da ke cikin kwaryar Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan siyasan PDP ne suka sankame albashin sojoji a aljifansu, inji gwamnatin Buhari

Ba a kai ga samun karin bayani daga Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar sojin ba.

A ‘yan watannin da suka gabata ana fama da hare-hare kan al’ummar Kaduna, ciki har da sansanonin sojojin Najeriya.

A watan Agustan 2021, wasu ‘yan bindiga sun kai hari makarantar horar da hafsoshin sojoji ta Najeriya (NDA), inda suka kashe jami’ai biyu.

Harin da aka kai har sansanin sojin ya zo ne kwanaki kadan bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan jirgin kasa a Kaduna, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jigatar wasu da dama.

Yadda NRC ta yi watsi da gargadin da aka yi mata kan shirin kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

A wani labari na daban, hukumar kula da ayyukan jirgin kasan Kaduna sun yi karin haske kan gazawar jami’ai a matakai daban-daban wajen dakile farmakin da aka kai wa jirgin kasa, wanda aka samu gargadi tun watanni da suka gabata.

Kara karanta wannan

'Yan Ta'adda Sun Ji Ba Daɗi Yayin Da Sojoji Suka Kashe Fiye Da 85 a Kaduna, Zamfara Da Borno

Wasikun da aka aike wa hukumomin tsaro da Daily Trust ta gani sun bayyana yadda aka bankado wannan makarkashiyar biyo bayan kutsen da jami’an leken asiri suka yi wanda ya kai ga fitar da sanarwar ga hukumomi daban-daban.

Manyan jami’an tsaro na zargin jami’an hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya NRC da kin bin shawarar da aka ba su na takaita zirga-zirgar jiragen kasa zuwa rana kadai banda dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel