Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC

Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC

  • Hukumar kula da jiragen kasa ta yi bayani kan yadda ake ci gaba da tuntubar lambobin wayan mutanen da suka bace a harin jirgin Abuja-Kaduna
  • Idan baku manta ba, a makon jiya ne wasu 'yan ta'adda suka farmaki jirgin kasan fasinja dauke da 'yan Najeriya da yawa
  • Lamarin ya haifar da tashin hankali, inda mutane suka shiga jimamin rashin sanin inda 'yan uwansu suke

Kaduna - Har yanzu ba a ji duriyar mutum dari da arba'in da shida cikin fasinjoji 362 da ke cikin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ba, kwanaki shida bayan harin da 'yan ta'adda suka kai kan jirgin.

Manajan daraktan hukumar kula da layin dogo ta Najeriya, Mista Fidet Okhiria ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka samo a ranar Litinin 4 ga watan Afirilu.

Kara karanta wannan

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

Barnar 'yan bindiga a jihar Kaduna
Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Rahoton Punch ya bayyana cewa, adadin fasinjojin da suka tsira ya karu zuwa 186 tun bayan harin na kwanakin nan.

Okhiria ya ce lambobin waya 51 da ke cikin takardar bayanan fasinjoji an same su a kashe ko kuma basa shiga tun da safiyar Talata yayin da lambobin waya 35 kuma suke shiga amma ba a daukar waya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma lura cewa lambobin waya 60 da ke cikin takardar lokacin da aka kira su, an gano babu su kwata-kwata.

Shugaban NRC ya fayyace cewa mutane 22 ne ‘yan uwansu suka shigar da rahoton batansu, sannan kuma an tabbatar da mutuwar mutane takwas.

Muna godiya ga jami'an tsaro, shugaban NRC

Hakazalika, ya kuma bayyana godiyarsa ga jami'an tsaro, kana yace za a ci gaba da sanar da bayanai masu amfani ga jama'a, inji rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye da bayanan mutanen da suka mutu a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

A cewarsa:

“Muna ci gaba da godiya ga jami’an tsaro kan duk wani goyon bayan da suka ba mu. Muna matukar godiya da ziyarar da Squadron Commander MOPOL 1 Kaduna ya kai a inda hatsarin ya faru a yau.
"NRC za ta ci gaba da sanar da jama'a game da abubuwan da ke faruwa don hana yada bayanan bogi da karya."

Gwamnati: Sunaye da lambar wayoyin mutum 398 da suka sayi tikitin jirgin Abuja zuwa Abuja

A wani labarin, gwamnatin jihar Kaduna ta saki takardar jerin sunayen fasinja na jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna mai suna AK9 wanda wasu ‘yan bindiga suka kai wa hari a daren ranar Litinin, 28 ga watan Maris.

A cewar Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na jihar Kaduna a wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, 30 ga watan Maris, ya ce takardar ta nuna cewa fasinjoji 398 ne suka sayi tikitin tafiya amma 362 daga cikin wadannan fasinjoji suka shiga jirgin.

Kara karanta wannan

Yadda Jami’an tsaro suka yi burus duk da an samu rahoton za a kai wa jirgin kasa hari

Wannan lamari ya tada hankalin jama'a saboda dangi da dama sun bayyana damuwa kasancewar basu ji labarin halin da 'yan uwansu ke ciki ba har zuwa yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel