Yanzu-Yanzu: Anga wata a wasu sassan kasar nan, inji kwamitin ganin wata

Yanzu-Yanzu: Anga wata a wasu sassan kasar nan, inji kwamitin ganin wata

  • Jim kadan bayan fitar da rahoton da cewa ba a jinjirin watan Ramadana a wasu jihohin Najeriya, yanzu kwamiti ya ce an ganshi a wasu
  • A daren Juma'a ne kwamitin ganin wata ya nemi musulman Najeriya su fara sanya ido domin duba jinjirin watan Ramadana
  • Gobe Asabar, 2 ga watan Afrilu ya tabbata 1 ga watan Ramadana a Najeriya idan Allah ya kaimu

A daren yau Juma'a ne a kwamitin ganin wata na kasa ya bukaci musulmai a Najeriya su fara duban jinjirin watan Ramadana.

Kwamitin ya bayyana cewa, ba a ga watan a wasu sassan Najeriya ba, amma a wasu sassan an gani, don haka gobe ta tabbata 1 ga watan Ramadana

Kwaminin ganin wata na kasa: Ba a ga wata a wasu jihohin Najeriya ba har yanzu
Kwaminin ganin wata na kasa: Ba a ga wata a wasu jihohin Najeriya ba har yanzu | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya bayyana haka ne a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindigan sun kai hari gidan Kwamishinan jiha, sun tada bama-bamai

A cewar bayanin baya da ke cewa ba a watan ba:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya zuwa yanzu babu rahotannin da aka samu daga Bauchi, Gombe, Azare, Misau, Numan, Lagos, Kaduna, Abuja, Bajoga, Nafada, Maiduguri da dai sauransu."

Kwamitin ya kuma nemi jama'a da su ba da bayani sahihi daga yankunansu game da ganin jinjirin watan na Ramadana.

An ga wata, inji kwamiti

Yanzu kuma kwamitin ya sanar da cewa, an samu ganin wata a wasu sassan kasar nan.

Yanzu dai ta tabbata gobe 1 ga watan Ramadana.

Sanarwar da kwamitin ya fitar ya ce:

Ramadana: A fara duban jinjirin wata daga ranar Juma'a, inji kwamitin ganin wata

A tun farko, kwamitin ganin wata na kasa (NMSC) ya sanar da cewa, lokaci ya yi da musulman Najeriya za su fara duban watan Ramadana a cikin wannan mako.

Kara karanta wannan

Dalilan Osinbajo na kin yarda Amaechi ya kashe N3.7b wajen tsare hanyar jirgin kasa

Wannan na zuwa ne yayin da musulman duniya ke ci gaba da shirye-shiryen fara Azumin Ramadana na shekara-shekara.

Sanarwar da kwamitin ya fitar a makon nan ta shafinsa na Facebook ya bayyana cewa, ranar Juma'a za ta kasance 29 ga watan Sha'aban na kalandar Islama, wanda ka iya zama ranar karshe na watan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel