Zamfara: Yan bindiga sun kai wani mummunan har kauyuka huɗu, sun halaka aƙalla mutum 17

Zamfara: Yan bindiga sun kai wani mummunan har kauyuka huɗu, sun halaka aƙalla mutum 17

  • Yan bindiga sun sake kai hari kauyukan karamar hukumar Anka a jihar Zamfara da tsakar rana, sun kashe akalla mutum 17
  • Wani mazaunin yankin, Hussaini, ya ce sun fito daga Sallar Azahar kenan suka hangi zuwan yan ta'addan, nan take suka yi takansu
  • A cewarsa, maharan sun tattara dabbobin jama'a a kasuwa, sun fasa shaguna sun ɗibi kayayyaki amfani na yau da kullum

Zamfara - Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 17 a wani hari da suka kai ƙauyuka huɗu na karamar hukumar Anka a jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce mutanen ɗauke da makamai sun farmaki ƙauyen Kadaddaba da tsakar rana, suka buɗe wa mutane wuta.

Sun bayyana cewa ba bu wani abu na tsokanar faɗa da yan kauyen suka yi da ya jawo yan ta'addan suka kai harin, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Neja: Yadda Kwale-Kwale ya nutse da mata da kananan yara yayin guduwa daga harin yan bindiga

An sake kai hari karamar hukumar Anka a Zamfara.
Zamfara: Yan bindiga sun kai wani mummunan har kauyuka huɗu, sun halaka aƙalla mutum 17 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazuani da ya faɗi sunansa da Hussaini a taƙaice, ya ce:

"Sun shigo a kan Mashina suka buɗe wa mutane wuta. Muna fitowa daga Sallan Azahar muka hangi tawagarsu na ƙarisowa, nan take muka ankarar da na kusa muka tsere jeji."
"Sun bi mutanen dake kokarin guduwa, duk wanda suka cimma su harbe shi, sun ƙashe mutum 10 a ƙauyen mu cikinsu har da sirikina. A Rafin Doka sun kashe mutum ɗaya, biyu a Babban Baye, a Wano kuma mutum huɗu."
"Ba wani nisa mutane suka yi ba, yanzu da nike magana da ku ina Anka na je gudun Hijira.'

Shin sun sace mutane ko wasu abubuwa?

Mutumin ya ƙara da cewa tun da farko yan bindigan sun shiga kasuwar Rafin Gero suka yi awon gaba da dabbobi da yawa waɗan da mutane suka kawo domin siyarwa.

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasan Kaduna-Abuja: Iyalan wasu matafiya na cikin firgici, har yanzu basu ji daga 'yan uwansu ba

"Sun kwance Shanu da sauran dabbobi suka tasa zuwa Jeji. Haka nan sun fasa shaguna sun ɗibi kayayyaki, akwai labarin da yace sun kashe mutane amma ban san adadin su ba."

Har yanzun da muke haɗa wannan rahoton ba'a samu jin ta bakin kakakin rundunar yan sanda na jihar, SP Muhammad Shehu, ba.

A wani labarin kuma Yan bindigan sun kai hari gidan Kwamishinan jiha, sun tada bama-bamai

Yan bindiga da ba'a gane su waye ba sun kai hari da abubuwan fashewa a gidan Kwamishinan Kwadugo na jihar Imo.

Kwamishinan ne ya tabbatar da haka da safiyar Jumu'a, ya ce babu wanda ya rasa ransa amma sun lalata gidan da Bam.

Asali: Legit.ng

Online view pixel