Da Duminsa: Mata da Kananan yara sun nutse a ruwa a kokarin tserewa mummunan harin yan bindiga a Neja

Da Duminsa: Mata da Kananan yara sun nutse a ruwa a kokarin tserewa mummunan harin yan bindiga a Neja

  • Kwale-Kwale ya kife da wasu yan gudun hijira akalla 20 yayin da suka tsere daga harin yan bindiga a yankin Munya ta jihar Neja
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa mutanen sun yi wa Jirgin ruwan yawa, sai da ya je tsakiyar ruwa ya kife
  • Mutanen da suka kunshi mata da ƙananan yara sun gudo ne daga ƙauyukan Guni da Kurgbaku

Niger - Aƙalla mutum 20 da suka ƙunshi mata da ƙananan yara ne suka nutse a cikin tafkin Guni-Zumba yayin da suke kokarin guduwa daga harin yan bindiga.

Daily Trust ta tattaro cewa Mutanen da suka nutse ɗin sun baro gidajen su ne lokacin da yan bindiga suka farmaki ƙauyukan Guni da Kurgbaku, ƙaramar hukumar Munya a jihar Neja.

Harin ya faru ne ranar Laraba da safe lokacin da yan bindigan suka mamaye ƙauyukan biyu, bisa tilas mazauna yankunan suka gudu domin tsira da rayuwa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sabon Shugaban APC ya dira Sakatariyar jam'iyya ta ƙasa, ya kama aiki gadan-gadan

Taswirar jahar Neja.
Da Duminsa: Mata da Kananan yara sun nutse a ruwa a kokarin tserewa mummunan harin yan bindiga a Neja Hoto: infotrustng.com
Asali: UGC

Wata majiya ta bayyana cewa Mutanen sun nutse ne a kan hanyar tsallake Tafkin zuwa sansanin yan gudun hijira dake Zumba da Gwada a cikin Kwale-Kwale.

Shehu Abubakar, wani mazaunin yankin ya shaida wa jaridar cewa kwale-kwalen ya ɗakko mutane fiye da ƙima, kuma hakan ya tilasta masa kifewa a tsakiyar kogin.

Punch ta rahoto Ya ce:

"Yan bindiga sun farmaki yankunan mu da safe, a kokarin guduwa wasu mutane suka kife a kogin Guni-Zumba, saboda nauyin mutane Kwale-Kwalen ya kife a tsakiyar ruwa."
"A yanzun, ba mu san adadin yawan mutanen da abun ya shafa ba saboda bamu samu nasarar tsamo ko mutum ɗaya ba. Amma zan iya cewa sun zarce 20, mata da yara na ciki."

Akwai ƙarancin jami'an tsaro

Abubakar ya koka cewa babu isassun jami'an tsaro da zasu kawo musu ɗauki a yankin baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Matasa sun fara lalata filin kwallon Abuja sakamakon kashin da Najeriya ta sha hannun Ghana

Wani mazaunin na daban, Michael Madaki, ya ce:

"Yan bindiga sun farmaki ƙauyen Guni a ƙaramar hukumar Munya ta jihar Neja, a kokarin mutane na guduwa Kwale-Kwale ya kife da su a tsakiyar ruwa."

Kakakin hukumar yan sanda reshen Neja, DSP Wasiu Abiodun, bai daga kiran waya ba kuma bai turo amsar sakonnin da aka tura masa ba kan lamarin.

A wani labarin kuma Jami'an hukumar EFCC Sun Cafke wani Kasurgumi ɗan Najeriya da Amurka ke nema ruwa a Jallo

Jami'an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta'adi sun yi ram da mutumin ne a karamar hukumar Orlu ta jihar Enugu.

FBI na zargin mutumin mai suna, Emmanuel Dike Chidiebere, da aikata damfara da halasta kuɗin haram a ƙasashen uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel