Harin jirgin kasan Kaduna-Abuja: Iyalan wasu matafiya na cikin firgici, har yanzu basu ji daga 'yan uwansu ba

Harin jirgin kasan Kaduna-Abuja: Iyalan wasu matafiya na cikin firgici, har yanzu basu ji daga 'yan uwansu ba

  • Wasu daga cikin ƴan uwan waɗanda farmakin jirgin ƙasan Kaduna ya ritsa dasu sun koka game da yadda basu samu cikakken bayani kan inda ƴan uwansu suka shiga ba
  • Sun ƙara da rokon gwamnatin jiha da ta saki jerin sunayen waɗanda suka samu raunuka, ko suka rasa rayukansu ko kuma aka yi garkuwa dasu
  • Duk da wani ma'aikaci a filin jirgin ƙasan ya ce, babu wanda zai iya cewa an yi garkuwa ko ba'a yi garkuwa da fasinjojin ba, saboda firgici ya sanya wasu daga cikin su tserewa cikin daji

Wasu daga cikin iyalan fasinjojin dake jirgin ƙasan da ƴan ta'adda suka tare a hanyar Kaduna, ranar Litinin sun ce har yanzu basu san halin da ƴan uwansu ke ciki ba, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wadanda suka jigata a harin jirgin Kaduna-Abuja

Yayin zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a tashar jirgin ƙasan Rigasa cikin Kaduna a ranar Talata, sun bayyana yadda har yanzu basu ji komai game da ƴan uwan nasu ba, bayan awa 14 da aukuwar mummunan lamarin.

Harin jirgin kasan Kaduna-Abuja: Iyalan wasu matafiya na cikin firgici, har yanzu basu ji daga 'yan uwansu ba
Harin jirgin kasan Kaduna-Abuja: Iyalan wasu matafiya na cikin firgici, har yanzu basu ji daga 'yan uwansu ba. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Saboda haka, suke roƙon gwamnatin jiha da ta kawo musu ɗauki don su samu sassauci game da fargabar da suke fuskanta.

Muhammad Barau, wani mazauni Anguwan Rimi a Kaduna, ya ce ya je filin jirgin don samun cikakken bayani game da aukuwar lamarin, inda ya kara da cewa, harin jirgin ƙasan ya ritsa da ƙaninsa.

"Mun kira layin wayarsa yafi a kirga, ba'a ɗagawa, sai dai daga bisani wani abokinsa dake tare dashi a jirgin kasan ya ɗaga ya shaida mana ɗan uwan nawa ya bar wayarsa a kan kujera, kuma bai san inda ya shiga ba.

Kara karanta wannan

Alwan Hassan, Manajan Daraktan BOA, ya yi batan dabo ta harin jirgin kasan Kaduna-Abuja

"Ya kamata a ce a yanzu gwamnati ta saki jerin sunayen mutanen da suka rasa rayukansu, waɗanda suka samu raunuka, da kuma yawan mutanen da gwannati ta ceta.
"A ƙalla idan aka yi hakan, zai sa hankalin mu ya kwanta, amma har yanzu bamu ji komai ba," a cewarsa.

Haka zalika, Lami Gombo, mai zama a Kidenden, cikin Kaduna, ta bayyana yadda har yanzu bata ji daga ɗan uwanta ba, wanda shima fasinja ne a jirgin ƙasan.

"Lambobin wayarsa a kashe suke; mun je asibitn sojin ƙasan Najeriya, amma bamu gan shi a can ba.
"Lamarin nada matukar tada hankali, saboda gaba daya iyalin sun kasa gane ko ɗan uwan nawa na da rai, ya mutu ne ko kuwa an yi garkuwa da shi," a cewarta.

Wasu da suka zanta da NAN sun bayyana damuwa kwatankwacin wannan, inda suka ƙara da cewa, hakalinsu ba zai taɓa kwanciya ba saboda yadda basu ji daga ƴan uwansun da harin ya ritsa dasu ba.

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasan Kaduna: Halin da dangin wadanda ke cikin jirgin ke ciki a yanzu

Wani ma'aikacin hukumar jirgin ƙasan Najeriya, wanda shima lamarin ya ritsa dashi, ya bayyana wa NAN yadda wasu fasinjoji suka faɗa cikin daji son tsira daga mummunan lamarin da ya auku.

"Babu wanda zai iya tabbatar da cewa an yi garkuwa da fasinjoji ko a'a, amma tashin hankalin ya sanya wasu mutane tserewa cikin daji don tseratar da rayukansu," a cewar ma'aikacin, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa.

Wasu da ake zargin ƴan ta'adda ne, sun kai wa jirgin ƙasan Kaduna, wanda ya baro Abuja karfe 6:00 na yammacin ranar Litinin, misalin karfe 7:45.

Kwamishinan tsaro da kula da lamurran cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, a ranar Talata, ya labarta yadda jami'an sojoji suka bawa jirgin ƙasan tsaro, sannan gwamnati ta ceto fasinjojin dake cikin shi.

Ya ce, KADSEMA da Nigeria Red Cross, na jihar Kaduna ne suka aiwatar da ceton.

Yayin da NAN ta tuntuɓi jami'in KADSEMA, wanda baya bukatar a ambaci sunansa, game da yawan waɗanda lamarin ya ritsa dasu, ya ce har yanzu suna cigaba da bincika hakan.

Kara karanta wannan

Harin Abuja-Kaduna: An fara gano yawan mutanen da suka mutu a harin jirgin ƙasan Kaduna

Sai dai, ayyukan jirgin ƙasa, waɗanda suka haɗa da sauran kasuwanci a tashar jirgin ƙasan Rigasa, Kaduna sun tsaya cak saboda aukuwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel