Babu komai tsakaninmu: Jita-jitar alakar soyayya tsakanin Momee Gombe da Hamisu Breaker

Babu komai tsakaninmu: Jita-jitar alakar soyayya tsakanin Momee Gombe da Hamisu Breaker

  • Jarumar fina-finan Kannywood ta bayyana gaskiyar alakarta da Hamisu Breaker, mawaki a masana'antar Kannywood
  • Ta bayyana haka ne yayin wata hira da aka yi da ita, inda tace sam babu alakar soyayya tsakaninta dashi
  • Momee Gombe, ta bayyana wakar da ta fi burge ta, inda tace wakar Jarumar Mata ta jawo mata suna a masana'antar Kannywood

Fitacciyar jarumar nan ta Kannywood, Maimuna Abubakar, wacce aka fi sani da Momee Gombe, ta bayyana cewa ba za ta taba mantawa da wakar Jarumar Mata ta fitaccen mawakin nan, Hamisu Sa’id Yusuf, wanda aka fi sani da Hamisu Breaker ba.

Mawakiyar ta kuma bayyana cewa yayin da wakar Jarumar Mata ta yi suna a cikin al'umma, wasu na ganin tana da alakar soyayya da Hamisu Breaker, wanda ta ce sam ba haka bane, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Abin da wanda ya kashe yarinya ta ya fada mana da mu ka hadu - Mahaifiyar Hanifa a kotu

Tsakanin Hamisu Breaker da Momee Gombe
Babu komai tsakaninmu: Jita-jitar alakar soyayya tsakanin Momee Gombe da Hamisu Breaker | Hoto: fimmagazine.com
Asali: UGC

Jarumar wadda aka haifa kuma ta tashi a jihar Gombe ta bayyana hakan ne a wata hira da BBC a ranar Alhamis yayin da take magana kan rayuwarta da kuma aikinta na wasan kwaikwayo.

Momee Gombe wadda ta fito a bidiyon wakar “Jarumar Mata”, ta yi suna, kuma ta jawo wasu na ganin akwai alakar soyayya tsakaninta da Breaker.

Sai dai Momee ta yi watsi da rade-radin cewa tana da alakar soyayya da mawakin, yayin da ta kuma bayyana cewa wakar ita ce ta fi so a duk wakoki kuma ba za ta taba mantawa da ita ba.

A cewarta:

“Mutane da yawa suna kirana da suna Jarumar Mata saboda wakar. Tabbas ina cikin wakar tare da abokin aikina Hamisu Breaker, sai mutane suka fara kirana da Jarumar Mata bayan hawa wakar.

Kara karanta wannan

Ta tabbata: Budurwar da ta yi wa Jaruma mai Kayan Mata kwacen miji, ta bayyana

“Ba zan taba mantawa da yadda na ji dadin wakar da ganin karbuwarta ba. Ban yi tunanin za ta samu karbuwa ba. Na kuma ji ana ta yayata cewa ina da soyayya da shi (Hamisu Breaker), amma a zahiri, wannan ba gaskiya ba ne. Kawai abokin aikina ne a masana’anta.”

Momee Gombe dai na daya daga cikin jaruman masana’antar Kannywood da ke tashe a yanzu. Ta fito a fina-finai da dama da suka samu karbuwa ciki har da Kishin Mata da Asalin Kauna.

Na taba soyayya da Fati Muhammed har maganar aure ya shiga tsakani amma abun bai yiwu ba – Lawan Ahmad

A wani labarin, shahararren jarumin Kannywood, Lawan Ahmad ya bayyana cewa ya taba soyayya da tsohuwar jarumar masana’antar, Fati Muhammad a shekarun baya.

Lawan ya ce a wancan lokacin har magana ta yi karfi tsakaninsu, domin manya sun shiga lamarin ana ta maganar aure.

Kara karanta wannan

Abin da wasu wadanda suka yi takara a APC suke fada, bayan sun sha kashi a zaben kasa

Sai dai kuma jarumin ya ce ana tsaka da maganar auren ne sai maganar ta wargaje domin Allah bai yi za su zama mata da miji ba. Ya kuma ce tun bayan ita bai kara soyayya da wata yar fim ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel