Na taba soyayya da Fati Muhammed har maganar aure ya shiga tsakani amma abun bai yiwu ba – Lawan Ahmad

Na taba soyayya da Fati Muhammed har maganar aure ya shiga tsakani amma abun bai yiwu ba – Lawan Ahmad

  • Jarumin Kannywood, Lawan Ahmad ya magantu a kan soyayyar da ya taba yi da tsohuwar jarumar masana'antar, Fati Muhammad
  • Lawan ya ce Allah bai yi zai auri Fati bane domin har maganar aure ta shiga tsakaninsu a wancan lokacin
  • Sai dai kuma, ya ce tun bayan ita, bai sake kulla soyayya da wata 'yar fim ba

Shahararren jarumin Kannywood, Lawan Ahmad ya bayyana cewa ya taba soyayya da tsohuwar jarumar masana’antar, Fati Muhammad a shekarun baya.

Lawan ya ce a wancan lokacin har magana ta yi karfi tsakaninsu, domin manya sun shiga lamarin ana ta maganar aure.

Na taba soyayya da Fati Muhammed har maganar aure ya shiga tsakani amma abun bai yiwu ba – Lawan Ahmad
Lawan Ahmad ya ce ya taba soyayya da Fati Muhammed har maganar aure ya shiga tsakani amma abun bai yiwu ba Hoto: NAIJASTICK/FimMagazine
Asali: UGC

Sai dai kuma jarumin ya ce ana tsaka da maganar auren ne sai maganar ta wargaje domin Allah bai yi za su zama mata da miji ba. Ya kuma ce tun bayan ita bai kara soyayya da wata yar fim ba.

Jarumin ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa wata tambaya da aka yi masa a wata hira a shirin ‘Daga bakin mai ita’ na BBC Hausa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

BBC ta tambaye shi ne kan ko ya taba soyayya da wata a masana’antar ta Kannywood, sai ya ce:

“Mun taba soyayya da Fati Muhammad wacce har maganar aure ma ta dan shiga tsakaninmu da ita, toh amma da yake ka san komai nufi ne na Ubangiji, a wancan lokacin Allah bai yi ba. Shikenan ita ce kadai muka yi soyayya da ita, amma daga ita gaskiya ban kara soyayya da wata ‘yar fim ba.”

Farin Jakada: Jarumin Kannywood Lawan Ahmad ya fito takarar siyasa a jihar Katsina

A gefe guda, mun ji cewa yayin da siyasar 2023 ke kara kusantowa, masu shirin tsayawa takarar wata kujera na cigaba da fito da kudirinsu fili tare da fara neman goyon bayan al'umma.

Ɗaya daga cikin jarumai a masana'antar shirya fina-finan Hausa Kannywood, Lawan Ahmad, ya sanar da shirinsa na neman takara a zaben 2023 dake tafe.

A wani rubutu da ya saki a shafinsa na Istagram, Lawan Ahmad, ya ce zai nemi takarar ɗan majalisar jiha mai wakiltar mazaɓar Bakori a majalisar dokokin Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel