Ta tabbata: Budurwar da ta yi wa Jaruma mai Kayan Mata kwacen miji, ta bayyana

Ta tabbata: Budurwar da ta yi wa Jaruma mai Kayan Mata kwacen miji, ta bayyana

  • Soshiyal Midiya ta gigice da labarin budurwar da ta yi wuff ta kwace mijin Jaruma mai Kayan Mata duk da kwarewarta a bada maganin mallaka
  • Kamar yadda budurwar ta wallafa a sashin labaranta na Instagram, ta nuna kauna ga tsohon mijin Jaruma, Fahad Isabor, inda shima ya mayar da martani
  • Jama'a sun sha mamakin wannan al'amarin duk da yadda mai Kayan Matan take dukan kirji kan yadda magungunanta ke tabbatar da mallakar miji

Fitacciyar mai siyar da kayan mata, Hauwa Saidu wacce aka fi sani da Jaruma, ta zama abun zunde da yafice bayan wata budurwa ta kwace mata mijinta.

Soshiyal midiya ta cika da labarin bayan sabuwar budurwar Ross Fahad Isabor, tsohon mijin Jaruma mai suna Jasmine London, ta bayyana kanta.

Ta tabbata: Budurwar da ta yi wa Jaruma mai Kayan Mata kwacen miji, ta bayyana
Ta tabbata: Budurwar da ta yi wa Jaruma mai Kayan Mata kwacen miji, ta bayyana. Hoto daga @ jarumaem pire
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Hana nuna wa duniya sallar Tarawih a Ramadana: Kungiyar Musulmai ta caccaki Saudiyya

Sau da yawa Jaruma kan bugi kirji tana fadin cewa ta san duk hanyoyin mallake miji ballantana da taimakon Kayan Mata da take siyarwa. Wannan lamarin ne yasa jama'a masu yawa suka sha mamakin yadda budurwar ta kwace mata miji cike da nasara.

Kwararriyar mai siyar da Kayan Mata ta fuskanci tangarda a aurenta wanda hakan yasa suka rabu salin alin ba tare da sanin kowa ba, hakan yasa take cigaba da bugun kirji kan kyan Kayan Matan ta.

Jasmine London ta je fannin labarinta na Instagram inda ta bayyana kaunarta ga tsohon mijin Jaruma, Ross Fahad Isabor.

Ta nuna godiyarta gare shi yayin da take kwatanta shi da haziki, mai tsoron Ubangiji, mai aiki tukuru da sauransu.

Ta rubuta: "@richrossfahad, haske na, kyakyawana, mai ilimi, mai kwazo da tsoron Ubangiji. Ba ka taba gazawa. Kana mayar da hankali a duk abinda za ka yi. Ina godiya gare ka a koda yaushe.

Kara karanta wannan

Tsakaninmu Ne: Magidanci Ya Faɗa Wa Ƴan Sanda Yayin Da Suke Tuhumar Matarsa Da Yunƙurin Datse Masa Mazakuta

A yayin martani ga wallafarta, Ross Fahad Isabor ya rubuta: "Nagode abar kauna, ina godiya da samun ki a rayuwata."

An samu rahotannin cewa a 2021 mijin Jaruma ya yi watsi da ita, amma ta karyata hakan

Jaruma mai Kayan Mata ta cigaba da wallafa bidiyoyin Regina Daniels, duk da uwar-watsin da aka yi a kotu

A wani labari na daban, fitacciyar ƴar Najeriyar wacce tayi suna a kafar sada zumuntar zamanin nan wurin siyar da kayan mata, Hauwa Saidu wacce aka fi sani da Jaruma, ta ci gaba da wallafa bidiyoyin jarumar Nollywood, Regina Daniels.

Yayin magana da masu amfani da yanar gizo, mai saida kayan matan ta cigaba da ɗora wallafar Regina Daniels a shafinta, duk da irin badaƙalar dake tsakanin su.

Jaruma ta wallafa bidiyonta da Regina a asibiti, lokacin da bata da lafiya inda take bata magani. Mai saida maganin matan ta cigaba da tallata hajarta mai bunkasa jindadi ga maaurata.

Kara karanta wannan

Maciya yake kirana: Mata ta kai kara gaban kotu, ta ce a raba ta da mijinta da ke gallaza mata

Asali: Legit.ng

Online view pixel