Abin da wanda ya kashe yarinya ta ya fada mana da mu ka hadu - Mahaifiyar Hanifa a kotu

Abin da wanda ya kashe yarinya ta ya fada mana da mu ka hadu - Mahaifiyar Hanifa a kotu

  • Mahaifiyar Hanifa Abubakar, Murja Suleiman Zubairu ta ba kotu labarin haduwarta da Abdulmalik Tanko
  • Murja Suleiman Zubairu mai shekara 38 ta ce malamin su Hanifa ya nuna bai san komai ba da aka tuntube shi
  • Abdulmalik Tanko ya zo har gida ya na kuka, ya na addu’a Allah ya sa a ga yarinyar da shi ya yi garkuwa da ita

Kano - Murja Suleiman Zubairu, wanda ita ce mahaifiyar Hanifa Abubakar ta bada labarin abin da ya faru tsakaninta da wanda ake zargi ya kashe mata ‘ya.

Daily Trust ta ce an gayyaci Murja Suleiman Zubairu a matsayin mutum na bakwai da ya gabatar da shaida a wannan shari’a da ake ta yi a kotu a jihar Kano.

Murja Zubairu mai shekara 38 a Duniya ta shaidawa Alkali yadda ta kai Marigayiya Hanifa makarantar Islamiyya a ranar Asabar, 4 ga watan Disamban 2021.

Kara karanta wannan

Amaechi: Dama na yi hasashen za a kawo hari a jirgi, na nemi kayan tsaro amma aka hana

Da kimanin karfe 5:30 da aka tashi karatu, sai wata yarinya a makwabta ta sheko gida ta shaida masu cewa wani mutumi ya yi gaba da Hanifa a Keke Napep.

Uncle ya dauke Hanifa - 'Yar makwabta

A cewar wannan yarinya da ta kawo labarin, da aka yi yunkurin a hana ta bin wannan mutumi, Hanifa ta shaida masu cewa malamin makarantar bokon su ne.

“Sai na tambayi wata cikin malamar da mu ke cigiyar Hanifa da ita ko akwai wani namijin malami bayan Abdulmalik a makarantar, domin duk malaman mata ne.”
Hanifa & Tanko
Hanifa Abubakar da Abdulmalik Tanko
Asali: Facebook
“Sai ta fada mani cewa akwai wani sabon malami namiji a makarantar, ko da aka tambaye shi, bai ma san wata Hanifa ba domin shi a sashen sakandare yake aiki.”
“Sai malamar nan ta kira Abdulmalik Tanko a wayar salula (kowa ya na jinsa), ta ba shi labarin malami ya dauke Hanifa, a lokacin sai ya ce ‘Subhanallahi’!"

Kara karanta wannan

APC ta shiga cikin hargitsi da Sanata Adamu su ka zama shugabannin jam’iyya na kasa

Abdulmalik Tanko ya rusa kukan karya

“A ranar Litinin da safe sai Abdulmalik ya zo gidanmu, ya na shigowa sai na fara kuka, mu na hada ido, sai ya fashe da kuka, har sai da ta kai ina ba shi hakuri.”
“Da zai tafi sai ya yi addu’a ga Ubangiji ya bayyana ta domin mu gan ta. A wannan lokacin sai mu ka daina zargin Abdulmalik saboda irin yadda ya yi a gabanmu.”

Daga nan malamin makaranta ya rika kokarin karbar kudin fansa a hannun iyayenta. A karshe dubunsa ta cika bayan ya kashe wannan yarinya mai shekara biyar.

Za su ba iyayen Hanifa kyautar 'yar su

Wani mutumi da ke zaune a garin Darazo a jihar Bauchi, Abdullahi Ahmed Latus ya ce idan iyayen Hanifa sun yarda, to zai ba su kyautar yarinyar cikinsa.

Idan za ku tuna, wannan mutum ya samu labarin kisan Hanifa, duk da ba su hada jini ko dangantaka ba, ya shirya mallakawa iyayen ‘yar da suka haifa.

Kara karanta wannan

Abin da wasu wadanda suka yi takara a APC suke fada, bayan sun sha kashi a zaben kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel