El-Rufai Ya Magantu Kan Harin Jirgin Kasa: Na Gargadi Gwamnatin Tarayya Ta Dena Jigilar Fasinjoji Da Daddare

El-Rufai Ya Magantu Kan Harin Jirgin Kasa: Na Gargadi Gwamnatin Tarayya Ta Dena Jigilar Fasinjoji Da Daddare

  • Bisa ga alamu ana yar nuna yatsa tsakanin hukumomin gwamnatin tarayya da na jiha game da harin da yan ta'adda suka kai wa jirgin kasa a Kaduna
  • Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce a baya, ya gargadi hukumomin gwamnatin tarayya game da yin tafiye-tafiyen dare a jirgin
  • A bangarensa, ministan sufuri na kasa, Chibuike Amaechi ya ce ya bukaci a samar da kayayyakin tsaro a baya

Jihar Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya yi gargadin a dena yin tafiyar dare da jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja.

El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana da wasu wadanda suka tsira daga harin da yan ta'adda suka kai wa jirgin kasan a ranar Litinin 28 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Gwamnati: Sunaye da lambar wayoyin mutum 398 da suka sayi tikirin jirgin Abuja zuwa Abuja

El-Rufai Ya Magantu Kan Harin Jirgin Kasa: Na Gargadi Gwamnatin Tarayya Ta Dena Jigilar Fasinjoji Da Daddare
Na Gargadi Gwamnatin Tarayya Ta Dena Jigilar Fasinjoji Da Daddare, In Ji El-Rufai. Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

A wata bidiyon da Television Continental ta wallafa, bayan sauraron wani fasinja, Malam El-Rufai ya ce:

"Ka sani ko, na fada wa ministan a dena tafiya da jirgin bayan karfe 5 na yamma. Na ce a dena amfani da jirgin na yamma. Domin mun san akwai yiwuwar a kai hari da dare."

Chibuike Rotimi Amaechi, tsohon gwamnan Jihar Rivers shine ministan da ke kula da sufuri.

"Fasinjan da ya fada wa gwamnan cewa yana aiki da hukumar jiragen kasa na Najeriya, NRC, ya tabbatar da cewa yan ta'addan sun sace mutane da dama."

Harin Jirgin Kasa: Shugaban Kungiyar Yan Kasuwan Najeriya Da Sakatare Suna Cikin Wadanda Aka Kashe

Kara karanta wannan

Amaechi: Dama na yi hasashen za a kawo hari a jirgi, na nemi kayan tsaro amma aka hana

A wani labarin, mambobin kungiyar ‘Yan kasuwan Najeriya, TUC, suna cikin wadanda harin da aka kai jirgin kasa ranar Litinin a Jihar Kaduna ya ritsa da su har suka rasa rayukansu.

Daily Trust ta tattaro yadda babban sakataren kungiyar TUC na kasa, Barista Musa-Lawal Ozigi da shugaban kungiyar na Jihar Kwara, Kwamared Akinsola Akinwunmi suka halaka sakamakon harin.

Wasu daga cikin mambobin kungiyar sun nuna rashin jin dadinsu dangane da harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel