Abun Kunya: Wani Magidanci ya ɗirka wa ɗiyarsa ciki har sau biyu, ya danna wa Matarsa saki

Abun Kunya: Wani Magidanci ya ɗirka wa ɗiyarsa ciki har sau biyu, ya danna wa Matarsa saki

  • Wani mutumi a jihar Legas ya ɗirka wa ɗiyar cikinsa juna biyu, ya zubar sannan ya ƙara mata wani cikin karo na biyu
  • Mahaifiyar yarinyar, wacce ta rabu da mutumin shekarun da suka shuɗe, ta fusata ta kai ƙorafinsa hannun yan sanda
  • Kakakin yan sanda, Benjamin Hundeyin, ya ce tuni suka cafke wanda ake zargi kuma zasu gudanar da bincike

Lagos - Wani Magidanci mai sana'ar hannu ɗan kimanin shekara 44, Mustapha Abiodun, yanzu haka yana tsare a kurkukun yan san da dake Caji Ofis na Ikeja bisa zargin ɗirka wa yarsa ciki.

Yarinyar wacce aka ɓoye sunanta ta fara rayuwa tare ɗa mahaifinta a yankin Alagbado, jihar Legas bayan iyayen sun rabu kuma ta koma hannun mahaifin tana shekara 14.

Vanguard ta rahoto cewa tun bayan komawarta gidan Mahaifin shekara biyu da suka shuɗe, ya fara amfani da ita.

Kara karanta wannan

Magidanci ya lakada wa tsohuwar matarsa da sirikarsa mugun duka a kan 'ya'yansu

Taswirar jihar Legas.
Abun Kunya: Wani Magidanci ya ɗirka wa ɗiyarsa ciki har sau biyu, ya danna wa Matarsa saki Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa lokacin da Mustapha ya fara lalata da ɗiyarsa ya bata hakuri bisa hujjar yana cikin Maye kuma ya ɗauki alƙawarin ba zai ƙara ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma hakan ba ta samu ba, alaƙar da ta shiga tsakanin su sai da ta yi sanadin ɗaukar cikin ɗiyar a watan Agusta, 2021, Lokacin da cikin ya cika wata huɗu Uban ya sa aka zubar da shi.

Bayan nasarar zubda cikin, Mutumin ya cigaba da holewarsa da cin zarafin yarinyar har ta sake samun ciki a karo na biyu.

A cewar wani maƙocin mutumin, Mustapha ya na da tsauri kan duk abinda ya shafi ɗiyarsa, baya barin tana harkokinta tare da mutanen Anguwa.

Yace idan ka cire lokacin da take zuwa makaranta da lokacin da take fita aiki, a koda yaushe suna tare da juna.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa kowace rana ake ƙara samun zaman lafiya a Najeriya, Gwamnatin Buhari ta magantu

Yace:

"Ba mu san akwai wani abu dake faruwa tsakanin su ba har sai lokacin da muka fahimci ta samu canji a jikinta."

Shin mahaifiyarta ta san abun da ke faruwa?

A cewar mahaifiyar yarinyar da abun ya faru a kanta:

"Tun tana wata uku na rabu da Mustapha, kuma tana tare da ni har zuwa shekara biyu baya lokacin da tace tana son ganin Ubanta kuma na haɗa su, daga nan ta koma hannunsa."
"Makonnin da suke wuce na samu kiran gaggawa cewa na zo na ɗauke 'yata. Lokacin da na iso Legas na tarar Mahaifin da yarinyar sun je Abeokuta wurin Jana'iza."
"Da suka dawo na gano cewa yarinyar na dauke da juna biyu saboda haka na gaggauta sawo yan sanda cikin lamarin."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin hukumar yan sanda na Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce sun kama wanda ake zargin ranar 20 ga watan Maris, 2022 bayan ƙorafin da Uwar ta shigar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Tsagin hamayya na kulla-kullan ruguza Najeriya' Gwamnatin Buhari ta fallasa sirrin

Yace a halin yanzun jami'an sashin jinsi na gudanar da bincike kan lamarin kafin ɗaukar mataki.

A wani labarin na daban kuma An fara gano yawan mutanen da suka mutu a harin jirgin ƙasan Kaduna

Wata majiya a kusa da tsahar jirgin ƙasa dake Rigasa Kaduna ta ce ana tsammanin fasinjoji Bakwai suka mutu a harin.

Tuni dai hukumar sufurin jiragen ƙasa ta kasa ta dakatar da jigila a hanyar biyo bayan harin da yan ta'adda suka kai wa jirgin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel