Magidanci ya lakada wa tsohuwar matarsa da sirikarsa mugun duka a kan 'ya'yansu

Magidanci ya lakada wa tsohuwar matarsa da sirikarsa mugun duka a kan 'ya'yansu

  • A karo na biyu, an zargi wani mutum da sake naɗawa tsohuwar matarsa da mahaifiyarta dukan kawo wuƙa, bayan sun kaiwa ƴaƴansa ziyara ba tare da izininsa ba
  • Saidai, tsohuwar matar ta bayyana yadda taje kaiwa yaranta kayan da zasu sanya a ranar bikin nuna al'adu a makaranta bayan yadda sukayi ta magiya da ta siya musu
  • Otarurhor ya musanta hakan, inda ya ce aurensu ya lalace ne saboda yadda matar ta gaza mishi biyayya, shiyasa ba yaso ta ziyarci yaransa ba tare da ta shaida mishi ba

An zargi wani mutum mai matsakaicin shekaru, Mr Thaddeus Otarurhor, ɗan asali kuma mazaunin Adagbrassa-Ogolo, cikin ƙaramar hukumar Okpe dake jihar Delta da naɗawa tsohuwar matarsa da surikarsa dukan kawo wuka, saboda kayan al'ada na makaranta da ta siyawa ƴaƴansu.

Otarurhor, yana ke da baƙar zuciya, gami da tarihin taɓa naɗawa tsohuwar matarsa da surikarsa duka, inda hakan yayi sanadiyyar rabuwar aurensu a shekarar 2019, ya sake rufarwa matan da basu da karfin kare kawunansu, saboda gangancin kawowa yaran kaya a ranar nuna al'adu na makarantarsu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Tsagin hamayya na kulla-kullan ruguza Najeriya' Gwamnatin Buhari ta fallasa sirrin

Magidanci ya lakada wa tsohuwar matarsa da sirikarsa mugun duka a kan 'ya'yansu
Magidanci ya lakada wa tsohuwar matarsa da sirikarsa mugun duka a kan 'ya'yansu. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

Vanguard ta ruwaito cewa, rikicin ya fara, yayin da yaran ke ƙarƙashin kulawar Otarurhors ya kira don sanarwa mahaifiyar game da ranar bayyana al'adu a makarantar yaran.

An gano yadda mahaifiyar yaran, wacce ta rabu da mijin nata, Miss Hope Epini, da farko ta ƙi amincewa da siyawa yaran tufafin, amma daga baya ta siya musu bayan naci da suka yi ta ma ta, wanda hakan ne ya canza ra'ayinta.

Saboda yadda ta san halin tsohon mijin nata da baƙar zuciyarsa, ta yanke shawarar zuwa gidan mahaifiyarta don ta bawa yaran kudi, kaya da kayan ƙarau.

Yayin jiran yaran, tsohon mijin nata ya tafi farfajiyar gidansu don kai kashedi, inda ya ja kunnenta da kada ta je kusa da farfajiyar gidan tsohon mijin nata yake zama.

Kara karanta wannan

Jaruma mai Kayan Mata ta cigaba da wallafa bidiyoyin Regina Daniels, duk da uwar-watsin da aka yi a kotu

Sai dai yayi barazana da cewa, idan ya ganta ko mahaifiyarta a wani guri kusa da ginin, dukkansu zasu ɗanɗana kuɗarsu.

An tattaro yadda Otarurhor, ya kara da yi musu zagin kare dangi, wanda ya tunzura ta har tayi kunnen uwar shegu da jan kunnenshi, duba da yadda tsohon mijin nata ke zaune a gidanta, sannan filin mallakin mahaifinta ne, Vanguard ta ruwaito.

Yayin zantawa da manema labarai daga baya, Hope Epini ta bayyana yadda daga zuwanta harabar gidan, Otarurhor ya harzuka da yadda ta ƙetare dokarsa, inda yayi hanzarin kai wa ita da mahaifiyarta farmaki , yayin da ya nannaushe ta.

Sai dai, da aka tuntubi Mr Thaddeaus Otarurhor, ya musunta zargin da ake masa, wanda ya siffanta su da zama marasa tunani. Ya ce, auren nasu ya taɓarɓare ne saboda matarsa bata mishi biyayya.

"Matsalar da na samu da tsohowar mata ta shi ne rashin min biyayya, kuma tana son mulkar gidan. Na ja kunnenta a kan kada ta kuskura ta ga yaran ba tare da ta fara kirana ba. Ba naso ta lalatamin tarbiyyar yara, amma taƙi. Wannan shine musabbabin rikicin, inda mahaifiyarta da wasu ƴan uwanta maza suka taɗa kai wajen faɗa dani," a cewarsa.

Kara karanta wannan

Yadda aka gano wata budurwa da aka yi garkuwa da ita tsawon shekara uku ɗauke da ciki wata 8

Asali: Legit.ng

Online view pixel