Labari mara dadi ga 'yan Najeriya: Ghana ta haramtawa Najeriya shiga gasar cin kofin duniya

Labari mara dadi ga 'yan Najeriya: Ghana ta haramtawa Najeriya shiga gasar cin kofin duniya

  • Najeriya dai ta sha kashi, ta rasa damar shiga gasar cin kofin duniya na 2022 saboda rashin cancanta
  • A yau ne Najeriya ta buga wasa da Ghana a filin kwallon Abuja, inda suka tashi kunnen dogi da ci 1-1
  • Wannan lamari dai ya jawo Ghana ta haramtawa Najeriya shiga gasar ta FIFA ta 2022 da za a kasar Qatar

Labari da dumi-dumi ya bayyana cewa, an tashi daga wasan share fagen shiga gasar kofin duniya da za a yi Qatar, wanda Super Eagles ta Najeriya ta buga da kasar Ghana a yau Talata.

Wannan na nuni da cewa, Najeriya ta fice daga gasar ta neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya a karshen wannan shekara, bayan da ta yi kunnen doki (1-1) da Ghana, inda ta sha kashi idan aka jimillar maki, inji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: 'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Hari Tashar Jirgin Kasa a Kaduna

Najeriya ta fita daga gasar neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya
Labari mara dadi ga 'yan Najeriya: Ghana ta haramtawa Najeriya shiga gasar cin kofin duniya | Hoto: vamguardngr.com
Asali: Twitter

Wannan shi ne karo ba biyu da Najeriya ta buga wasa da Ghana, inda a bakon jiya 'yan wasan Najeriya suka yi tattaki zuwa kasar Ghana, kamar yadda muka ruwaito a baya.

Maimakon Najeriya, wannan ya nuna cewa, Ghana ce za ta samu shiga gasar ta FIFA 2022 da za buga a Qatar bana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A baya, fitaccen dan kwallon kafan Super Eagles; Ahmed Musa ya yiwa 'yan Najeriya alkawarin tabbatar da lallasa Ghana domin samun dama shiga gasar.

Matasa sun fusata a filin wasa

Wasu matasa yan Najeriya da suka je kallon kwallon Najeriya da Ghana a filin kwallon Moshood Abiola dake birnin tarayya Abuja sun fusata, sun haukace.

Wani dan jaridan Ghana, Yaw, ya dauki bidiyon matasa da yammacin nan sun bazu cikin filin kwallon bayan waje da Najeriya da kasar Ghana tayi kuma ta hanata zuwa gasar kwallon duniya a Qatar bana.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe wani Dirakta a hukumar NBTE, yana cikin jirgin kasa Abuja-Kaduna

Bidiyon ya nuna jami'an tsaron sun harba barkonon tsohuwa don tarwatsa matasan amma da alamun abun ya yi kamari.

Alkawarin Ahmed Musa ga 'yan Najeriya: Za mu lallasa Ghana domin shiga gasar cin kofin duniya na 2022

A wani labarin, Ahmed Musa ya bayyana cewa ‘yan wasan kwallon kafan Najeriya; Super Eagles za su yi iya kokarinsu wajen ganin sun gamsar da ‘yan Najeriya ta hanyar samo tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022, inda ta alkawarta lallasa Ghana.

Kyaftin din na Super Eagles ya ce 'yan wasan Najeriya sun yi nadamar rashin tabuka abin a zo a gani a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Senegal ta lashe watannin baya, Sports Brief ta tattaro.

Musa da yake zantawa da tashar Youtube ta hukumar kwallon kafa ta Najeriya ya yi gargadin cewa wasan da Super Egales za ta buga tsakaninta da Black Stars zai kasance mai wahala saboda hamayyar da ke tsakanin Najeriya da Ghana.

Kara karanta wannan

Hotunan El-Rufai Da Mataimakiyarsa Sun Ziyarci Wadanda Harin Da Yan Bindiga Suka Kai Wa Jirgin Kasa Ya Ritsa Da Su

Asali: Legit.ng

Online view pixel