Alkawarin Ahmed Musa ga 'yan Najeriya: Za mu lallasa Ghana domin shiga gasar cin kofin duniya na 2022

Alkawarin Ahmed Musa ga 'yan Najeriya: Za mu lallasa Ghana domin shiga gasar cin kofin duniya na 2022

  • Ahmed Musa ya yi alkawarin cewa Super Eagles za ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2022 domin share hawayen 'yan Najeriya bayan faduwa a gasar AFCON
  • Kyaftin din na Super Eagles ya amince wasan da za su buga da Ghana gabanin gasar cin kofin duniya ba zai zama mai sauki ba saboda fafatawa tsakanin kasashen biyu
  • Ghana za ta karbi bakuncin Super Eagles a wasan farko na damar shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Kumasi a ranar Juma'a 25 ga Maris

Ahmed Musa ya bayyana cewa ‘yan wasan kwallon kafan Najeriya; Super Eagles za su yi iya kokarinsu wajen ganin sun gamsar da ‘yan Najeriya ta hanyar samo tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022, inda ta alkawarta lallasa Ghana.

Kara karanta wannan

Sheikh El-Zakzaky: Jami'an Tsaro Sun Buƙaci Matata Ta Tuɓe Tufafinta

Kyaftin din na Super Eagles ya ce 'yan wasan Najeriya sun yi nadamar rashin tabuka abin a zo a gani a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Senegal ta lashe watannin baya, Sports Brief ta tattaro.

Ahmed Musa ya yiwa 'yan Najeriya alkawarin shigar Super Eagles gasar cin kofin Duniya
Alkawarin Ahmed Musa ga 'yan Najeriya: Za mu lallasa Ghana domin shiga gasar cin kofin duniya na 2022 | Hoto: Lars Baron
Asali: Getty Images

Musa da yake zantawa da tashar Youtube ta hukumar kwallon kafa ta Najeriya ya yi gargadin cewa wasan da Super Egales za ta buga tsakaninta da Black Stars zai kasance mai wahala saboda hamayyar da ke tsakanin Najeriya da Ghana.

Super Eagles ta Najeriya da Black Stars ta Ghana

Yanzu haka dai Super Eagles din na can a otal din Wells Carlton da ke Abuja a shirinta na fafata wasa da Black Stars da ‘yan wasa 18 tuni a sansanin kungiyar.

Ghana za ta karbi bakuncin Super Eagles din a filin wasanta na Baba Yara da ke Kumasi a ranar Juma'a mai zuwa, 25 ga Maris bayan an sauya wurin wasan na farko daga filin wasan Ghana na Accra saboda rashin kyawunsa.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari da Gwamnoni suka karbo bashin Naira Tiriliyan 6.64tr a cikin shekara daya

Kocin Ghana ya hakikance cewa Black Stars za su iya lallasa Super Eagles

A halin da ake ciki, mataimakin kocin Ghana, George Boateng ya yi imanin cewa Black Stars na kasar ta Ghana sun shirya tsaf don samun damar tsallakewa zuwa gasar cin kofin duniya da za a taka a kasar Larabawa; Qatar.

A cewar kafar yada labaran wasanni ta Complete Sports, Boateng ya bayyana cewa kungiyar ta kwallon kafa na da kyakkyawan shiri don lallasa Super Eagles lokacin da kungiyoyin biyu za su kara a Kumasi a ranar Juma'a, 25 ga Maris.

Ghana na neman tsallakewa zuwa gasar cin kofin duniya karo na 4 yayin da Super Eagles kuwa ke neman shiga gasar a karo na 7.

Bayan shekaru kusan 30, Buhari ya tuna da Super Eagles, ya cika alkawarin da aka yi masu

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta amince da rabon gidaje ga tsofaffin ‘yan wasan kwallon kafa da suka bugawa kasar Najeriya shekaru 28 da suka wuce.

Kara karanta wannan

Kudi sun samu: Najeriya ta sayar da danyen mai na N14.4trn a 2021 ga wasu kasashe 5

Premium Times ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya dauki nauyin cika alkawarin da aka yi wa wadannan ‘yan kwallon kafa 22 a tun a wancan lokacin.

Wani jawabi daga ma’aikatar ayyuka da gidaje na kasa ya tabbatar da cewa Mai girma shugaban kasa ya amince a raba gidajen ga tsofaffin taurarin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel