Yan bindiga sun kashe wani Dirakta a hukumar NBTE, yana cikin jirgin kasa Abuja-Kaduna

Yan bindiga sun kashe wani Dirakta a hukumar NBTE, yana cikin jirgin kasa Abuja-Kaduna

  • Har yanzu, sunayen wadanda harin yan ta'adda ya rutsa da su jirgin Abuja zuwa Kaduna na bayyana
  • Kawo yanzu hukuma ta bayyana cewa mutum takwas ne suka rasa rayukansu a wannan mumunar hari
  • An tabbatar da mutuwar Dirakta a hukumar NBTE kuma tuni an garzaya da shi mahaifarsa don jana'iza

Wani diraktan hukumar ilmin ayyukan hannu NBTE, Abdu Isa Kofarmata, ya rasa rayuwarsa ranar Litinin a harin da yan bindiga suka kai jirgin kasan Abuja-Kaduna.

Daily Nigerian ta ruwaito wani dan uwan mamacin da cewa Diraktan ya mutu ne sakamakon harbin bindigan da ya sha lokacin harin.

A cewar majiyar, an garzaya da gawarsa jihar Kano don jana'iza.

Marigayin ya mutu yana mai shekaru 55 kuma ya bar mata guda, da 'yaya hudu

Dirakta a hukumar NBTE
Yan bindiga sun kashe wani Dirakta a hukumar NBTE, yana cikin jirgin kasa Abuja-Kaduna Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Obi na Onitsha: Amsa waya ya hana ni hawa jirgin Abuja zuwa Kaduna da aka kai wa farmaki

Harin Jirgin Ƙasa: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Ɗakko Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya lashi takobin yin hayar sojoji daga kasashen ketare don su taya yaki da ‘yan ta’adda bayan harin da suka kai wa jirgin kasa a Kaduna ranar Litinin.

Ya kuma lissafo jihohi 4 na yankin arewa maso yamma, inda ya ce akwai yuwuwar su bi sahun shi. Jihohin sun hada da Zamfara, Kebbi, Katsina da Sokoto.

Ya ce zasu dauki wannan matakin ne matsawar gwamnatin tarayya bata dauki wani matakin a zo a gani ba a yankin.

El-Rufai ya shaida wa manema labaran cikin gidan gwamnati hakan, bayan ya kai wa shugaba Muhammadu Buhari ziyara har fadarsa don sanar da shi batun sabbin hare-heren.

Asali: Legit.ng

Online view pixel