'Karin Bayani: 'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Hari Tashar Jirgin Kasa a Kaduna

'Karin Bayani: 'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Hari Tashar Jirgin Kasa a Kaduna

  • Wasu bata gari da ake kyautata zaton yan fashin daji ne suka kai hari tashan jirgin kasa na Gidan kan layin dogo na Abuja-Kaduna
  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan fashin dajin sun saka wasu abubuwan fashewa (bam) a kan layin dogon hakan ya saka jirgin ya tsaya dole
  • An tabbatar da sace mutane takwas cikin fasinjojin yayin da wasu da dama kuma har yanzu ana nemansu ba a gansu ba

Jihar Kaduna - 'Yan ta'adda sun kai hari tashan jirgin kasa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, Channels Television ta ruwaito.

Majiyoyi sun ce yan ta'adda sun saka bam ne a kan layin dogon hakan ya tilasta wa jirgin da ya baro Abuja zuwa Kaduna ya dakata, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnati: Har yanzu ba a san adadin mutanen da harin jirgin kasa Abuja-Kaduna ya shafa ba

Yanzu-Yanzu: 'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Hari Tashar Jirgin Kasa a Kaduna
'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Hari Tashar Jirgin Kasa a Kaduna. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

Wannan shine hari na biyu da yan ta'addan ke kai wa a hanyar ta Kaduna zuwa Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalla mutane bakwai ne suka rasu sakamakon harin da yan ta'addan suka kai a kauyen Dutse a ranar Litinin.

Harin jirgin kasa na biyu a Kaduna: Na yi matukar kaduwa da samun labari, Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna bakin ciki kan harin da yan bindiga suka kai kan jirgin kasan Kaduna wanda ya yi sanadiyar mutuwa da raunata mutane da dama a ranar Litinin, 28 ga watan Maris.

A ranar Talata, 29 ga watan Maris, shugaban kasar ya ce harin ya yi masa ciwo sosai, wanda shine na biyu da aka kai a baya-bayan nan.

Buhari ya yi Allah-wadai da tayar da jirgin kasan fasinjojin, inda ya bayyana shi a matsayin abun damuwa matuka, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Matasa sun fara lalata filin kwallon Abuja sakamakon kashin da Najeriya ta sha hannun Ghana

Harin jirgin kasa: Osinbajo ya soke tafiyarsa zuwa Lagas don taron ‘Birthday’ din Tinubu, ya tafi Kaduna don yin jaje

A gefe guda, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya isa jihar Kaduna, yan sa’o’i kadan bayan harin ta’addanci da aka kai kan jirgin kasa da ke dauke da fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna.

Kakakin mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande, ya ce ubangidan nasa na a hanyarsa ta zuwa Lagas domin halartan taron ‘birthday’ din Tinubu amma sai ya karkata akalar tafiyar tasa zuwa Kaduna bayan ya samu labarin irin barnar da harin ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel