Hotunan El-Rufai Ya Ziyarci Wadanda Harin Da Yan Bindiga Suka Kai Wa Jirgin Kasa Ya Ritsa Da Su

Hotunan El-Rufai Ya Ziyarci Wadanda Harin Da Yan Bindiga Suka Kai Wa Jirgin Kasa Ya Ritsa Da Su

  • Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna tare da mukarrabansa sun ziyarci wasu daga cikin wadanda harin yan bindiga a jirgin kasa ya shafa
  • Gwamnan na Kaduna ya kai ziyarar ne asibitin sojoji na 44 da kuma asibitin Saint Gerald da ke unguwar Kakuri a birnin Kaduna domin jajantawa mutanen
  • Ita ma mataimakiyar gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe ta kai irin wannan ziyarar na jajantawa mutanen da suka raunata sakamakon harin yan bindigan a jirgin kasa

Jihar Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ziyarci mutanen da harin da yan bindiga suka kai wa jirgin kasa a ranar Litinin ya ritsa da su.

Gwamnan ya jagoranci wasu jami'an gwamnati zuwa asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna da kuma asibitin Saint Gerald inda wasu mutanen ke jinya, kamar yaddaya wallafa a shafinsa na Twitter.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin Kasa: Shugaban Kungiyar Yan Kasuwan Najeriya Da Sakatare Suna Cikin Wadanda Aka Kashe

Daily Trust ta rahoto yadda yan ta'addan suka kasa bam a titin jirgin wanda ya taso daga Abuja yana kan hanyarsa na zuwa Kaduna.

Yayin da an bindige wasu fasinjojin, wasu kuma an yi awon gaba da su.

Kazalika, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dr Hadiza Balarabe, a safiyar ranar Talata ta ziyarci asibitin St. Gerald da ke Kakuri Kaduna domin duba wasu da suka jikkata sakamakon harin jirgin kasan.

Ga wasu hotunan a kasa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hotunan El-Rufai Ya Ziyarci Wadanda Harin Da Yan Bindiga Suka Kai Wa Jirgin Kasa Ya Ritsa Da Su
El-Rufai ta tawagarsa sun ziyarci wadanda harin yan bindiga ya ritsa da su. Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

Hotunan El-Rufai Ya Ziyarci Wadanda Harin Da Yan Bindiga Suka Kai Wa Jirgin Kasa Ya Ritsa Da Su
Gwamna Kaduna ya ziyarci wadanda yan bindiga suka kai wa hari a jirgin kasa. Hoto: @GovKaduna.
Asali: Twitter

Hotunan El-Rufai Ya Ziyarci Wadanda Harin Da Yan Bindiga Suka Kai Wa Jirgin Kasa Ya Ritsa Da Su
Gwamnan Kaduna da tawagarsa yayin ziyarar da suka kai wa wadanda harin yan bindiga a jirgin kasa ya ritsa da su. Hoto: @GovKaduna.
Asali: Twitter

Hotunan El-Rufai Ya Ziyarci Wadanda Harin Da Yan Bindiga Suka Kai Wa Jirgin Kasa Ya Ritsa Da Su
Gwamn El-Rufai Ya Ziyarci Wadanda Harin Da Yan Bindiga Suka Kai Wa Jirgin Kasa Ya Ritsa Da Su. Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

Harin Jirgin Kasa: Shugaban Kungiyar Yan Kasuwan Najeriya Da Sakatare Suna Cikin Wadanda Aka Kashe

A bangare guda, Mambobin kungiyar ‘Yan kasuwan Najeriya, TUC, suna cikin wadanda harin da aka kai jirgin kasa ranar Litinin a Jihar Kaduna ya ritsa da su har suka rasa rayukansu.

Daily Trust ta tattaro yadda babban sakataren kungiyar TUC na kasa, Barista Musa-Lawal Ozigi da shugaban kungiyar na Jihar Kwara, Kwamared Akinsola Akinwunmi suka halaka sakamakon harin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya soke taron 'Birthday' dinsa don nuna jimamin harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Wasu daga cikin mambobin kungiyar sun nuna rashin jin dadinsu dangane da harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel