Harin Jirgin Kasa: Shugaban Kungiyar Yan Kasuwan Najeriya Da Sakatare Suna Cikin Wadanda Aka Kashe

Harin Jirgin Kasa: Shugaban Kungiyar Yan Kasuwan Najeriya Da Sakatare Suna Cikin Wadanda Aka Kashe

  • Mambobin kungiyar ‘yan kasuwan Najeriya, TUC, suna cikin wadanda suka halaka sakamakon harin da aka kai wa jirgin kasa a Kaduna ranar Litinin
  • An samu bayanai akan yadda babban sakataren kungiyar, Barista Musa-Lawal Ozigi da shugaban kungiyar a Kwara, Kwamared Akinsola Akinwunmi suka rasa rayukansu
  • Wasu mambobin kungiyar sun bayyana alhininsu dangane da babban rashin da kungiyar ta tafka, kamar yadda suka bayyana wa manema labarai

Jihar Kaduna - Mambobin kungiyar ‘Yan kasuwan Najeriya, TUC, suna cikin wadanda harin da aka kai jirgin kasa ranar Litinin a Jihar Kaduna ya ritsa da su har suka rasa rayukansu.

Daily Trust ta tattaro yadda babban sakataren kungiyar TUC na kasa, Barista Musa-Lawal Ozigi da shugaban kungiyar na Jihar Kwara, Kwamared Akinsola Akinwunmi suka halaka sakamakon harin.

Kara karanta wannan

Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Harin Jirgin Kasa: Shugaban Kungiyar Yan Kasuwan Najeriya Da Sakatare Suna Cikin Wadanda Aka Kashe
Harin Jirgin Kasa: Shugaban TUC Da Sakatare Suna Cikin Wadanda Aka Kashe. Hoto: The Cable/Daily Trust.
Asali: Twitter

Wasu daga cikin mambobin kungiyar sun nuna rashin jin dadinsu dangane da harin.

Wata majiya daga TUC wacce ta tattauna da wakilin Daily Trust ta wayar salula, ta shaida cewa:

“Mun yi rashin babban sakatare da kuma shugabanmu na Jihar Kwara.”

Sai da ‘yan bindiga suka dasa abu mai fashewa a titin jirgin kasa

Daily Trust ta ruwaito yadda ‘yan ta’addan suka sanya abu mai fashewa a kan titin jirgin kasan. Hakan yasa jirgin da ya taso daga Kaduna zuwa Abuja ya tsaya cak da misalin karfe 6 na yamma.

Bayan nan, sun bude wa fasinjoji wuta, inda suka halaka wasu yayin da suka yi garkuwa da wasu.

Dangane da labarin yadda ta kaya, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya ce an gano gawawwaki 8 sannan mutane 26 sun samu raunuka amma suna asibiti ana kulawa da lafiyarsu.

Kara karanta wannan

Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wadanda suka jigata a harin jirgin Kaduna-Abuja

A cewarsa kamar yadda rahoto ya nuna daga hukumar jirgin kasan Najeriya, mutane 362 ne suka hau jirgin.

'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Hari Tashar Jirgin Kasa a Kaduna

A wani labarin, 'yan ta'adda sun kai hari tashan jirgin kasa na da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, Channels Television ta ruwaito.

Majiyoyi sun ce yan ta'adda sun saka bam ne a kan layin dogon hakan ya tilasta wa jirgin da ya baro Abuja zuwa Kaduna ya dakata, Nigerian Tribune ta rahoto.

Wannan shine hari na biyu da yan ta'addan ke kai wa a hanyar ta Kaduna zuwa Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel