Harin Jirgin ƙasa: Ku shiga daji ku yi ruwan bama-bamai kan maɓoyar yan ta'adda, Majalisa ga Sojoji

Harin Jirgin ƙasa: Ku shiga daji ku yi ruwan bama-bamai kan maɓoyar yan ta'adda, Majalisa ga Sojoji

  • Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci sojojin Najeriya na sama da ƙasa su ragargaza maɓoyan yan ta'adda a ko ina suke
  • Wannan na zuwa ne biyo bayan harin baya-bayan nan da suka kai kan jirgin ƙasa a hanyar Kaduna-Abuja
  • Majalisar ta kuma roki shugaba Buhari ya ayyana cikakken yaƙi da yan ta'adda domin tsaftace ƙasar nan

Abuja - Majalisar Dattawa ta yi kira ga rundunar sojin ƙasa da sama, su gaggauta, tarwatsa maɓoyar yan bindiga da nufin dawo da zaman lafiya a sassan Najeriya.

Majalisar ta yi wannan kiran ne ranar Talata biyo bayan cimma matsaya kan kudirin duba, "Yawaita kai hari kauyuka da kayayyakin gwamnati a jihar Kaduna."

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Uba Sani, shi ne ya ta da maganar a zaman Majalisar kuma Sanatoci suka tafka mahawara, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Harin Abuja-Kaduna: An fara gano yawan mutanen da suka mutu a harin jirgin ƙasan Kaduna

Majalisar dattawa da yai.magana kan harin Kaduna.
Harin Jirgin ƙasa: Ku shiga daji ku yi ruwan bama-bamai kan maɓoyar yan ta'adda, Majalisa ga Sojoji Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Sanatan ya ce:

"Harin baya-bayan nan da yan ta'addan suka kai sun halaka kusan mutum 50, sun sace wasu sama da 100 a kauyuka kusan 10 na gundumar Yakawada a ƙaramar hukumar Giwa."
"Ba su tsaya iya nan ba, suka kai hari Filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa dake Kaduna. Duk da ba su ji da daɗi ba a hannun jami'an tsaro amma sun kashe mutum ɗaya."
"Yayin da mutane ke shirin farfaɗowa daga wannan ta'addanci na kisan yan uwan su a mako ɗaya, yan ta'adda suka sake dawo wa."

Bugu da ƙari, Sanatan ya kuma taɓo harin da yan bindiga suka kai wa jirgin ƙasa a hanyar Abuja-Kaduna a dai-dai Kateri – Rijana, Kilomita kaɗan kafin karisa wa tashar Rigasa.

Sani ya ƙara da cewa dazukan da waɗan nan yan ta'addan ke zama ba wasu ɓoyayyu bane kuma mutane a shirye suke su taimaka da bayanai.

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: IGP da Shugaban Sojoji zasu je wurin da yan bindiga suka ɗana wa Jirgi Bam a Kaduna

A nasa bamgaren, Sanata Ɗanjuma Laah, ya ce matukar ba'a dauki mataki ba, nan gaba yan ta'addan nan masu rike da mukamai ne zasu zama babban abin harin su.

Wane matakin majalisa ta ɗauka?

Majalisar dattawan, a matsayar da ta cimma ta roki shugaba Buhari, ya ayyana cikakken yaƙi da yan ta'adda domin tsaftace kowane ɓangaren kasar nan daga sharrin su, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Ta kuma roki Sojojin ƙasa da na Sama sun ragargaza maɓoyan yan ta'addan da nufin ganin bayansu da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowane yankuna.

Sanatocin sun kuma bukaci hukumonin tsaro su ɗauki tsauraran matakai domin kare faruwar haka nan gaba.

Ta kuma ƙara da cewa, cikin gaggawa Sojoji su sa ido a kan sabbin gine-gine da ake gudanarwa a filin jirgin Nnamdi Azikiwe Airport, Abuja.

Daga nan kuma sai Majalisar ta gudanar da shiru na tsawon Minti ɗaya domin ta'aziyya ga mutanen da suka rasu a harin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa kowace rana ake ƙara samun zaman lafiya a Najeriya, Gwamnatin Buhari ta magantu

A wani labarin kuma NRC ta dakatar da sufurin jirgin kasan Abuja- Kaduna har ila ma sha'a Allahu

Hukumar sufurin jiragen kasa a Najeriya watau NRC ta sanar da dakatar da sufurin fasinjoji a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna har sai lokacin da hali yayi.

Wannan ya biyo bayan harin Bam da yan bindiga suka kaiwa jirgin daren Litinin a tsakanin garin Kateri da Rijana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel