Da duminsa: Mun dakatar da sufurin jirgin kasan Abuja-Kaduna har ila ma sha'a Allahu, NRC

Da duminsa: Mun dakatar da sufurin jirgin kasan Abuja-Kaduna har ila ma sha'a Allahu, NRC

  • Bayan harin ranar Litinin, hukumar NRC ta dakatad da jigilar fasinjoji a jirginta na Abuja zuwa Kaduna
  • Hukumar ya fitar da labarin don tabbatar da harin da yan ta'adda suka kaiwa jirgin ranar Litinin
  • Kawo yanzu akalla mutum takwas ake fargabar sun rasa rayukansu yayinda daruruwan suka bace

Legas - Hukumar sufurin jiragen kasa a Najeriya watau NRC ta sanar da dakatar da sufurin fasinjoji a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna har sai lokacin da hali yayi.

Wannan ya biyo bayan harin Bam da yan bindiga suka kaiwa jirgin daren Litinin a tsakanin garin Kateri da Rijana.

Jirgin kasan Abuja-Kaduna
Da duminsa: Mun dakatar da sufurin jirgin kasan Abuja-Kaduna har ila ma sha'a Allahu, NRC
Asali: UGC

Hukumar NRC ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita da safiyar Talata, 29 ga Maris, 2022.

Kara karanta wannan

Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC

Tace:

"Ya ku fasinjoji, sakamakon wasu dalilai da bamu yi zato ba. An dakatar da sufurin jirgin Kaduna-Abuja."
"Duk yadda ta kaya zamu sanar da ku."

Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC

Har yanzu ba a ji duriyar mutum dari da arba'in da shida cikin fasinjoji 362 da ke cikin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ba, kwanaki shida bayan harin da 'yan ta'adda suka kai kan jirgin.

Manajan daraktan hukumar kula da layin dogo ta Najeriya, Mista Fidet Okhiria ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka samo a ranar Litinin 4 ga watan Afirilu.

Rahoton Punch ya bayyana cewa, adadin fasinjojin da suka tsira ya karu zuwa 186 tun bayan harin na kwanakin nan.

Okhiria ya ce lambobin waya 51 da ke cikin takardar bayanan fasinjoji an same su a kashe ko kuma basa shiga tun da safiyar Talata yayin da lambobin waya 35 kuma suke shiga amma ba a daukar waya.

Kara karanta wannan

Sifeto Janar IGP Alkali ya yi sintiri titin Abuja-Kaduna, ya zuba jami'an tsaro

Asali: Legit.ng

Online view pixel