Sabon hari: 'Yan bindiga sun sake kai hari jihar Neja, sun sace mutane sama da 40

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sake kai hari jihar Neja, sun sace mutane sama da 40

  • Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki yankin jihar Neja, sun sace Rabaran da wasu mutane sama da 40
  • Wannan na zuwa jim kadan bayan da gwamnati ta karfafi gwiwar mazauna kan komawa yankunansu
  • Rahotanni sun tattaro cewa, kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihar Neja ta tabbatar da faruwar lamarin

jihar Neja - Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki Neja jiya Lahadi sun yi awon gaba da limamin cocin Katolika na Cocin St Mary da ke Sarkin Pawa, hedikwatar karamar hukumar Munya ta Jihar Neja, Rabaran Leo Raphael Ozigi da wasu mutanen kauyen 44.

Daily Trust ta ce ta samu labarin cewa, an yi garkuwa da Rabaran ne a hanyarsa ta zuwa Gwada daga Sarkin Pawa a lokacin da ya ci karo da ‘yan bindiga da ke barna, inda suka yi taho-mu-gama da shi tare da wasu mutanen kauyen.

Kara karanta wannan

An yankewa wacce ta raba man fetur a taro hukuncin watanni 27 a gidan yari

'Yan bindiga sun yi barna a Neja
Sabon hari: 'Yan bindiga sun sake kai hari jihar Neja, sun sace mutane sama da 40 | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sakataren kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Neja, Fasto Raphael Opawoye, ya tabbatar da sace Rabaran Ozigi.

A cewarsa:

"An yi garkuwa da Rabaran Dr Leo Raphael Ozigi ranar Lahadi a hanyarsa ta komawa Gwada daga Sarkin Pawa bayan hidimar bautar ta ranar Lahadi."

Sakataren karamar hukumar Munya, James Jagaba, ya bayyana sabon barnar ‘yan bindiga a karamar hukumar Munya a matsayin abin takaici.

Yace:

“Ilahirin hukumar Munya tana cikin tashin hankali. Halin da ake ciki a yankin yana da ban tsoro. Ana yin garkuwa da mutane a dukkan sassan kananan hukumomin.”

An sace wasu mutane 44 a yankin

Wani mazaunin yankin mai suna Shehu Abubakar, ya shaida wa Daily Trust cewa wasu mutanen kauyen 44 da aka sace na daga cikin wadanda suke koma yankunansu daga sansanonin ‘yan gudun hijira a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Da dumi: Jihar Kaduna ta sake daukar dumi yayin da yan bindiga suka kashe mutum 50, sun yi awon gaba da wasu

A cewarsa:

"Muna cikin damuwa saboda da alama matsalar mu ba ta kare ba. Jama’a sun fara dawowa ranar Asabar don shirin noman doya.
“Gwamnati ta karfafe mu mu koma ga yankunanmu cewa za a yi shirye-shiryen magance tsaro. A ranar Asabar ne mutane suka fara dawowa kuma wadannan miyagu sun sake farmakarmu.”

Abubakar ya koka da yadda ‘yan bindigan da ke cin karensu ba babbaka tun ranar Asabar suke barna a hanyar Sarkin Pawa zuwa Gwada tare da garken shanun da suka yi awon gaba da su a lokacin da suke kai hare-hare kan mazauna.

Kaduna: Baya ga hari a masallaci, 'yan bindiga sun hallaka mutane, sun sace wasu mata

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kan titin Fumigi da ke Unguwan Galadima, Gonin-Gora, cikin karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, sun kashe mazauna tare da sace wasu mata biyu.

Mataimakin shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Arewa, Rabaran John Hayab ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun bindige Shahararren ɗan kasuwa har Lahira

Hakan na zuwa ne kwanaki uku da sace wani limamin cocin Katolika, Rabaran Joseph Akete na cocin St. John Catholic, Kudenda da ke karamar hukumar Kaduna ta Kudu.

Haka kuma, cikin mako guda, ‘yan bindiga sun kashe mutane biyar, tare da kona wata tankar mai a kauyen Manini, kusa da Kuriga, a kan babbar hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna.

'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun kashe babban Basarake a kan hanyar zuwa gaida mara lafiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel