Yan bindiga sun shiga har gida, sun bindige wani Shahararren ɗan kasuwa har Lahira a Jalingo

Yan bindiga sun shiga har gida, sun bindige wani Shahararren ɗan kasuwa har Lahira a Jalingo

  • Wasu yan ta'adda sun bi dare sun kutsa cikin gidan wani babban dillalin shanu a Jalingo, jihar Taraba, sun kashe shi
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun kuma tasa iyalansa. matarsa da 'ya'yansa guda biyu zuwa sansanin su da ba'a sani ba
  • Hukumar yan sanda na jihar Taraba ta tabbatar da faruwar Lamarin, kuma tuni aka yi wa mamacin Jana'iza da safiyar Alhamis

Taraba - Wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun halaka wani fitaccen dillalin shanu kuma suka sace matarsa da ƴaƴansa maza biyu a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Sanannen ɗan kasuwan, Alhaji Gidado Hassan, shi ke jagorantar kasuwancin shanu a birnin Jalingo, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Yan bindiga sun kashe ɗan kasuwa a Taraba.
Yan bindiga sun shiga har gida, sun bindige wani Shahararren ɗan kasuwa har Lahira a Jalingo Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa maharan sun farmake shi ne a gidansa dake kauyen Mallam Audu da misalin ƙarfe 2:00 na daren ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun halaka dan kasuwa, sun sace matarsa da yaransa

Haka nan, Rahoto ya nuna cewa yan bindigan da suka kai adadin mutum 12 sun kutsa gidan ɗan kasuwan da wannan dare.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alhajin ya rasa rayuwarsa ne yayin da makasan ke kokarin tilasta masa da iyalansa zuwa wani wuri da ba'a sani ba.

An gudanar da Jana'iza ga mamacin kuma aka binne shi a maƙabartar Jika Da Dari da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar yau Alhamis.

Hukumar yan sandan Taraba ta tabbatar da lamarin

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da kisan sanannen ɗan kasuwna ga manema labarai.

Jihar Taraba na ɗaya daga cikin jihohin Arewa ta tsakiya dake fama da matsalar masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

A wani labarin mai kama da wannan Yan bindiga sun kashe babban Basaraken gargajiya a Filato

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: 'Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom Takarar Shugabancin Ƙasa

Yan bindiga sun halaka Basaraken gargajiya a jihar Filato, yayin da yake kan hanyar zuwa gaida mara lafiya a Asibiti.

Wani mazaunin yankin ya ce tuni aka ɗakko gawarsa aka mata jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel