Yanzu-Yanzu: Jami'an gidan gyaran hali sun shirya a kotu domin tafiya da Abba Kyari
- Bayan hana ba da belin DCP Abba Kyari da sauran jami'an da ake zargi da harkallar miyagun kwayoyi, an tura su magarkama
- An ce jami'an gidan gyaran hali tuni sun shirya tsaf domin tafiya da Abba Kyari da kuma wani jami'i zuwa gidan gyaran hali na Kuje
- Hakazalika, sauran jami'an da ake zargi na shida da na bakwai za a kaisu gidan gyaran hali da ke Suleja
Labarin da ke iso mu yanzun nan ya bayyana cewa, tuni ma’aikatan gidan gyaran hali na Kuje suka isa babban kotun tarayya, inda ake sauraraan shari'ar Abba Kyari da NDLEA.
Bidiyon da TVC ta yada ya ce, Mista Kyari da sauran jami’an ‘yan sanda za a ajiye su a gidan yari na Kuje, yayin da wanda ake kara na shida da na bakwai za a kai su gidan gyaran hali na Suleja.
Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da kai ruwa rana kan batun Abba Kyari da zargin da ake masa tare da wasu jami'ai kan kulla harkallar miyagun kwayoyi.
Kalli bidiyon:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A halin da ake ciki, Mai shari’a Nwite ya ba da umarnin a gaggauta kammala shari’ar wadanda ake kara, kamar yadda ta sanya ranar 28 ga watan Afrilu domin sake duba hujjojin da suka shafi mutum biyu da suka amsa laifinsu a tun farko, inji rahoton Vanguard.
Idan baku manta ba, Umeibe da Ezenwanne; wadanda ake tuhuma na shida da na bakwai a zargin, a ranar 7 ga watan Maris, lokacin da aka gurfanar da su tare da DCP Kyari, sun amsa laifin aikata laifin safarar miyagun kwayoyi da ake tuhumar su da su.
A ranar Litinin din da ta gabata ne kotun ta saurari bahasi daga bangaren masu gabatar da kara da kuma na tsaro, kan bukatar da NDLEA ta gabatar na sake duba hujjojin da ake tuhumar su biyun, domin samun damar yanke musu hukunci daidai da laifinsu.
Kotu ta ki amincewa da ba da belin DCP Abba Kyari
A wani labarin, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar neman belin da DCP Abba Kyari da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Sunday J. Ubua suka shigar.
Idan baku manta ba ana tuhumarsu da laifukan da suka shafi harkallar muggan kwayoyi tare da wasu mutane biyar, The Nation ta ruwaito.
Mai shari’a Emeka Nwite, a wani hukunci da ya yanke a safiyar yau Litinin, ya ce masu gabatar da kara sun gabatar da isassun hujjoji a gaban kotu domin nuna kin amincewa da belin manyan jami’an ‘yan sandan biyu.
Asali: Legit.ng