Maciya yake kirana: Mata ta kai kara gaban kotu, ta ce a raba ta da mijinta da ke gallaza mata

Maciya yake kirana: Mata ta kai kara gaban kotu, ta ce a raba ta da mijinta da ke gallaza mata

  • Wata matar aure ta garzaya Kotun gargajiya a Abuja ta nemi a raba aurenta saboda yana gallaza mata
  • Matar mai suna Patience Ibrahim ta ce mijin nata na kiranta da macijiya daga aljannan ruwa
  • Sai dai mijin ya roki kotun da ta yi watsi da bukatun matar tasa bayan ya ki amsa zargin da take masa

Abuja - Wata matar aure mai suna Misis Patience Ibrahim, a ranar Alhamis ta maka mijinta, Mista Talpha Atega, a gaban wata kotun gargadiya da ke Jikwoyi, Abuja, kan zargin kiranta da macijiya.

A korafinta, Patience ta fada ma kotun cewa Atega na yawan kiranta da ‘macijiya daga aljanun ruwa’, baya ga kin sauke hakokin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na mijinta, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tsakaninmu Ne: Magidanci Ya Faɗa Wa Ƴan Sanda Yayin Da Suke Tuhumar Matarsa Da Yunƙurin Datse Masa Mazakuta

Maciya yake kirana: Mata ta kai kara gaban kotu, ta ce a raba ta mijinta da ke gallaza mata
Maciya yake kirana: Mata ta kai kara gaban kotu, ta ce a raba ta mijinta da ke gallaza mata Hoto: Thisday
Asali: UGC

Patience ta ce:

“Mijina ya ki daukar dawainiyan gida a matsayinsa na miji kuma uba; ni ke yin komai-aikin gida, biyan kudin haya, ciyarwa da sauransu.
“Da nayi masa magana kan lamarin, sai ya fara zagina; ya ce ni macijiya ce daga aljanun ruwa.
“Ina so a rabamu; ba zan iya ci gaba da rayuwa da mutum da ke wannan tunanin a kaina ba.”

Ta kuma roki kotu da kada ta mikawa mijin nata ragamar kula da da daya tilo da suka haifa, saboda tarbiyarsa.

Ta nuna tsoron cewa dan na iya daukar munanan dabi’u daga gare shi.

Sai dai, da yake kare kansa, wanda ake kara, Mista Atega, ya karyata dukkanin zarge-zargen sannan ya roki kotu da kada ta amsa bukatun matarsa.

Alkalin kotun, Mista Labaran Gusau, ya dage sauraron lamarin har zuwa ranar 30 ga watan Maris, don yanke hukunci, rahoton Pulse.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Matar aure ta haifa ɗan jaki, ta bada labarin yadda tayi dakon cikin na shekara 2

Zuciyata ta daina ƙaunar mijina, Matar Aure ta nemi Kotun Musulunci ta raba auren

A wani labarin, kotun Shari'ar Musulunci dake zamanta a Anguwar Magajin Gari, Kaduna, ranar Litinin, ta amince da bukatar wata matar Aure, Rakiya Ladan, na raba aurenta bisa hujjar ta dena kaunar mijinta.

Alƙalin Kotun Mai shari'a Nuhu Falalu, shi ne ya gimtse igiyoyin auren wanda ya shafe shekara 9, kamar yadda Jaridar Daily Trsut ta rahoto.

Alƙalin Kotun ya kuma umarci Magidancin mai suna Abba, ya bar matar ta zo ta kwashe karikitanta baki ɗaya daga cikin gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel