Da Ɗumi-Dumi: 'Yan bindiga sun kai hari hedkwatar yan sanda a Imo, sun yi ɓarna

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan bindiga sun kai hari hedkwatar yan sanda a Imo, sun yi ɓarna

  • Yan bindiga sun kai mummunan hari wata Hedkwatar yan sanda a Imo, mutane yankin sun tsorata sun yi takan su
  • Wani mazaunin yankin ya ce Artabun da aka yi tsakanin dakarun yan sanda da maharan ya hargitsa mutane kamar duniya ce zata tashi
  • Kakakin rundunar yan sanda na jihar Imo, Abattam, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yace zai kara bincikawa

Imo - Da safiyar Litinin, wasu ƴan bindiga sun farmaki hedkwatar yan sanda dake Otoko, ƙaramar hukumar Obowa a jihar Imo dake kudancin Najeriya.

Jaridar Punch ta tattaro cewa yan ta'addan sun bar jami'an yan sanda biyu kwance da rauni yayin harin.

Mazauna ƙauyen sun shaida wa manema labarai cewa maharan sun shigo da karfe 3:00 na dare, kuma sun kwashe dogon lokaci yayin harin.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan Sanda Sun Cafke Ɗaya Cikin Manyan Kwamandojin Shugaban 'Yan Bindiga Bello Turji

Yan bindiga sun farmaki yan sanda a Hedkwata.
Da Ɗumi-Dumi: 'Yan bindiga sun kai hari hedkwatar yan sanda a Imo, sun yi ɓarna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto Wani Mutumi ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bamu iya bacci ba da dare, ƙarar tashin makamai babban tashin hankali ne. Yayin da mutane da yawa suka tsere cikin jeji, wasu kuma sun fake a cikin gidajen su."
"Hedkwatar yan sandan tana kan babbar hanyar Owerri-Umuahia, dakarun yan sanda sun tarbe su, suka fara artabu, komai ya ƙara dagulewa mutanen ƙauyen kai kace duniya ce zata tashi."
"An yi kazamin musayar wuta da bamu taɓa gani ba, yan sanda biyu sun ji munanan raunuka, yanzu haka an gaggauta kai su Asibiti."

Maharan sun kwashi kashinsu a hannu

Wata majiya ta daban ta bayyana cewa jami'an tsaro sun samu nasarar fatattakar yan bindiga kuma ba su samu damar shiga harabar hedkwatar yan sandan ba.

"Yan bindigan sun fuskanci turjiya daga yan sandan dake bakin aiki, ba su iya shiga harabar ba, an yi artabu mai muni. Yan sanda biyu sun jikkata, bansan halin da suke ciki ba."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An sanar da Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC, Hotuna

"Yanzu da nake magana da ku, an girke jami'an tsaro ta ko ina a yankin. Mutane a tsorace suke, kowa ya yi muƙus a cikin gida, abun dai ba daɗin ji."

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Imo, Micheal Abattam, da aka tuntuɓe shi yace, "Eh dagaske ne an kai hari," amma ya yi alkawarin fitar da karin bayani daga baya.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari Kaduna, sun tattara maza da mata 47

Yan ta'adda sun kai hari ƙauyen Agunu Dutse dake ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna da tsakar daren Alhamis.

Bayanai daga mazauna yankin sun nuna cewa maharan sun jikkata wani da harbi, sun kuma yi awon gaba da mutum 47.

Asali: Legit.ng

Online view pixel