Kaduna: Kwastam Ta Kama Babban Motar Maƙare Da Naman Jaki Da Ganyen Wiwi

Kaduna: Kwastam Ta Kama Babban Motar Maƙare Da Naman Jaki Da Ganyen Wiwi

  • Hukumar kwastam a Jihar Kaduna ta kwace naman jaki cikin wata babbar mota da kayan shaye-shaye katan 12 masu kimar N250,000,000
  • A ranar Juma’a hukumar ta bayyana hakan inda ta ce cikin wata daya rak ta samun wadannan tarin nasarorin, sannan ta kwace wasu kwayoyi
  • Shugaban hukumar na Zone B, Albashir Hamisu ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a garin Kaduna

Kaduna - A ranar Juma’a, hukumar kwastam ta shaida yadda ta kwace wata babbar mota cike taf da naman jaki da buhunhunan kayan maye masu kimar fiye da N250,000,000 a cikin wata daya, The Punch ta ruwaito.

Yayin tattaunawa da manema labarai a Kaduna, shugaban hukumar na Zone “B” Kaduna, Albashir Hamisu, ya bayyana yadda aka boye buhunhunan kayan maye 2,348 da dauri 126 na wasu masu kimar N251,701,000,000.

Kara karanta wannan

Da dumi: Jihar Kaduna ta sake daukar dumi yayin da yan bindiga suka kashe mutum 50, sun yi awon gaba da wasu

Kaduna: Kwastam Ta Kwace Naman Jaki Cike da Babbar Mota, Da Sauran Kayan Maye
Kaduna: Kwastam Ta Kwace Naman Jaki Cike Da Babbar Mota, Da Ganyen Wiwi. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Hamisu ya bayyana hakan ne inda ya ce tsakanin ranar 24 ga watan Fabrairu da 23 ga watan Maris na shekarar 2022, sun kwace makamantan hakan sau 144.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Punch ta bayyana yadda ya lissafo sauran abubuwan da suka kwace inda ya ce akwai ledoji 3,700 na tramadol da ledoji 460 na kwayar D6.

Bayan kwace kwayoyin, sun mika su ga hukumar NDLEA

A cewarsa, masana sun tabbatar da cewa kwayar D5 kamar tramadol ta ke, kuma sun mika su hannun hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA.

Ya ce sun kwace miyagun kwayoyin ne a lokacin babu jami’an NDLEA a kusa. Saboda hadin kan da ke tsakanin hukumomin yasa suka mika musu kwayoyin.

A cewar jami’in:

“Sauran abubuwan da suka kwace sun hada da buhunhuna 1,100 na shinkafa masu nauyin 50kg, ababen hawa na hannu guda 7, kayan sawa na hannu dauri 128, ababen hawa cike da kayan sumogal da kuma dauri kashi 100 na kyallaye.

Kara karanta wannan

EFCC ta saki tsohon gwamna bayan kwashe kwana 6 a hannunta, ta kwace fasfotinsa

“Hukumar ta kwace buhunhuna 13 cike da takalma, katan 514 na taliyar kasar waje, katan 18 na madara ta kamfanin Milky Creamer da katan 11 na biskit.”

Hamisu ya hori jama’a akan su kasance masu fallasa miyagun ayyuka a kusa da su

Shugaban hukumar ya lissafo galan 65 na mangyada na kasar waje, galan 319 na Premium Motor Spirit da buhunhuna 336 na taba da sauran su.

Ya ce sun kama wani da ake zargin yana da alaka da naman jakin kuma tuni an mika shi ga rundunar ‘yan sanda a Kaduna don ci gaba da bincike da kuma daukar mataki.

Hamisu ya ce NCS za ta ci gaba da yin iyakar kokarin ta na gyara Najeriya. Kuma ta yi kira ga ‘yan Najeriya na kwarai inda ya ce su kasance masu bin doka da kuma bayar da bayanai akan ‘yan sumogal.

Kwastam Ta Kama Motar Dangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250

Kara karanta wannan

NDLEA ta kwace wiwi mai nauyin 374.397kg daga masu safara a jihar Kano

A wani rahoton, Kwantrolla Janar na Kwastam, Team A Unit, Mohammed Yusuf, ya ce jami'an hukumar sun kwace wata motar babban Dangote makare da buhun shinkafa na kasar waje 250 da aka haramta shigo da su.

Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Ikeja, Legas, yayin taron manema labarai inda ya bada jawabin ayyukan da suka yi cikin makonni hudu a sassa daban-daban, The Punch ta ruwaito.

Ya bayyana cewa a cikin kayan da aka kwace akwai kwantena ta katako mai tsawon kafa 20; buhunan shinkafa masu nauyin 50kg guda 1000; taya na gwanjo guda 3,143; kunshin tufafin gwanjo 320; Buhun fatar jaki 44 da ganyen wiwi kilogiram 137.3.

Asali: Legit.ng

Online view pixel