Zamfara: 'Yan Sanda Sun Cafke Ɗaya Cikin Manyan Kwamandojin Shugaban 'Yan Bindiga Bello Turji

Zamfara: 'Yan Sanda Sun Cafke Ɗaya Cikin Manyan Kwamandojin Shugaban 'Yan Bindiga Bello Turji

  • Yan sanda a Jihar Zamfara sun yi nasarar cafke Abdullahi Umar, wanda aka fi sani da Sangamere, daya cikin manyan yaran shugaban yan bindiga Bello Turji
  • An kama Sangamere ne a yayin da yan sandan ke wata bincike mai zurfi game da garkuwa da wata mata mai shekaru, 60, Hajiya Inno da aka sace
  • A halin yanzu rundunar yan sandan ta ce tana zurfafa bincike domin gano sauran abokan harkallarsa kafin daga bisani a gurfanar da shi a gaban kotu ya girbi abin da ya shuka

Zamfara - Rundunar yan sandan Jihar Zamfara ta ce ta kama daya cikin kwamandojin hatsabibin shugaban yan bindiga Bello Turji, Abdullahi Umar da aka fi sani da 'Sangamere' sun kuma ceto wata yar shekaru 60, Hajiya Inno.

Da aka holen wanda ake zargin a hedkwatar yan sanda a Gusau a ranar Asabar, kwamishinan yan sanda ta bakin kakakin yan sanda, SP Shehu Mohammed ya ce yan sandan sun samu nasarori sosai a jihar, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Dan sanda ya halaka rayuka 2 yayin da ya yi kokarin tserewa daga masu kama shi a Bauchi

Zamfara: 'Yan Sanda Sun Cafke Daya Cikin Manyan Kwamandojin Bello Turji.
'Yan Sanda Sun Cafke Daya Cikin Manyan Kwamandojin Bello Turji a Zamfara. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Twitter

A cewarsa yan sandan sun dakile harin yan bindiga, sun kashe daya, sun kwato AK-47, Babur Boxer, Sun kama mutum 10 wadanda ake zargi da laifuka, sun kuma ceto wata yar shekaru 60 a Jihar.

Ga wani sashi cikin jawabinsa:

"A ranar 20 ga watan Maris na 2022, Tawaga ta musamman na yaki da yan bindiga da ke sintiri a yankin Gwashi a karamar hukumar Bukuyum, ta kama hatsabibin shugaban yan bindiga, Lawali Ruguduma, na karamar hukumar Batsari.
"Yayin masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, ya ce yana cikin yan bindigan da ke adabar Jihohin Sokoto, Zamfara da Katsina. Ana cigaba da bincike don gano abokan harkallarsa kafin a kai su kotu."

Yan sanda sun kama kwamandan Turji yayin bincike

Kara karanta wannan

Na yi mankas da kwayoyi kafin in zaneta: Matashin Bakano da ya halaka kakarsa, ya jefa gawarta a rijiya

Ya cigaba da cewa kafin hakan, sun samu korafi kan sace wata mai shekaru 60, Hajiya Inno na Gambanda Magero a karamar hukumar Gumi a ranar 21 ga watan Maris na 2022, sun kama aiki.

"Yan sanda sun yi bincike mai zurfi inda suka ceto wanda aka yi garkuwar suka kama mutum takwas da ake zargi ciki har da kwamandan hatsabibin dan bindiga Bello Turji," in ji Mohammed.

A halin yanzu suna tsare ana cigaba da zurfafa bincike.

Kwamishinan yan sandan ya yi kira ga al'ummar jihar su rika yaba kokarin yan sandan su kuma cigaba da addu'an samun zaman lafiya a Zamfara da Najeriya.

'Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ke Kai Wa 'Yan Bindigan Neja Abinci

A wani rahoton, Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 20, Umar Dauda wanda ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a jihar, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi: Jihar Kaduna ta sake daukar dumi yayin da yan bindiga suka kashe mutum 50, sun yi awon gaba da wasu

A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, an samu bayani akan yadda aka kama matashin bayan mazauna yankin sun bayar da bayanan sirri ga hukuma.

Kamar yadda takardar tazo:

“An yi kamen ne a ranar 16 ga watan Maris din 2022, da misalin karfe 11 na dare bayan samun bayanan sirri akan yadda ake yawan ganin wani mai kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a kauyen Kapako da ke Lapai.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel