Sokoto: 'Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 4 Saboda 'Sun Ƙi Yarda Shanu Su Cinye Amfanin Gonarsu'

Sokoto: 'Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 4 Saboda 'Sun Ƙi Yarda Shanu Su Cinye Amfanin Gonarsu'

  • Wasu miyagun yan bindiga sun halaka wasu manoma hudu a Gatawa, karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto
  • Majiyoyi sun bayyana cewa yan bindigan sun nemi manoman su sayar masu kayan gonarsu ne kafin su girbe amma ba su yarda ba
  • Hakan yasa yan bindigan suka gayyato wasu abokansu suka taho a kan babura suka yi wa manoman kawanya suka hallaka su

Sokoto - Yan bindiga sun kashe wasu hudu yankin Gatawa a karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

Daily Trust ta rahoto cewa yan bindigan sun halaka manoman ne a cikin gonarsu.

Sokoto: 'Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 4 Saboda 'Sun Ƙi Yarda Shanu Su Cinye Amfanin Gonarsu'.
'Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 4 a Sokoto Saboda 'Sun Ƙi Yarda Shanu Su Cinye Amfanin Gonarsu'. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar 'yan sa-kai na Sabon Birni ya tabbatar da afkuwar harin

Shugaban kungiyar yan sa-kai a Sabon Birni, Musa Muhammad (wanda aka fi sani da Blacky), ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa maharan sun kaiwa manoman harin ne misalin karfe 4.30 na yammacin Laraba.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun kashe babban Basarake a kan hanyar zuwa gaida mara lafiya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mutanen yankin sun yi tsamanin an sace su ne sai yau da safe da aka gano gawarwakinsu," in ji shi.

Wadanda suka riga mu gidan gaskiyan sune Safiyanu Usman, Ya'u Girmu da Ashiru.

Wata majiyar ta ce an kai musu harin ne saboda mutanen sun ki sayar da amfanin gonarsu ga yan bindigan.

"Suna son su siya kayan gonar ne domin dabobinsa amma manoman ba su amince ba.
"Don haka suka gayyaci mutanensu daga wasu wuraren. Sun taho a kan babura, suka zagaye manoman sannan suka kashe su," a cewar majiyar.

Sai dai, ba a samu ji ta bakin kakakin rundunar yan sandan Jihar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar, ba domin wayarsa tana kashe.

An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona

A bangare guda, wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.

Kara karanta wannan

Bayan Lallasa Su, An Zaga Gari Da Wasu Matasa 4 Da Aka Kama Dumu-Dumu Suna 'Satar' Kaji a Gidan Gona

Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.

Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel