Minista sukutum da guda ya tare a birnin Abuja saboda tsabar 'tsoron' Gwamnan jiharsa

Minista sukutum da guda ya tare a birnin Abuja saboda tsabar 'tsoron' Gwamnan jiharsa

  • Tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi ya ce a yanzu hankalinsa ya na Abuja ne ba gida ba
  • Rt. Hon. Amaechi ya ce a halin da ake ciki, Abuja ya zama gidansa tun da Nyesom Wike ke kan mulki
  • A cewar Amaechi, Gwamnansa yanzu shi ne Mai girma Ministan harkokin birnin tarayya na kasa

Abuja - Tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi ya shaidawa Duniya cewa yana jin tsoron gwamna mai-mulki a halin yanzu a jiharsa Nyesom Wike.

Jaridar Daily Post a ranar Lahadi, 27 ga watan Maris 2022, ta rahoto Chibuike Rotimi Amaechi yana bayanin yadda dole ta sa ya tare a birnin tarayya Abuja.

Da ake hira da Chibuike Rotimi Amaechi a gidan talabijin, an yi masa tambaya kan taimakawa jam’iyyar APC ta karbe mulki daga hannun PDP a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Ainihin abin da ya sa Gwamnan Anambra ya nemi ya shilla Amurka a ranar da ya bar ofis

Babban Ministan sufurin kasar sai ya nuna cewa ba zai iya zuwa gida (jihar Ribas) ba, ya ce hankalinsa a zaben 2023 zai tattaru ne a nan (garin Abuja).

“Yanzu nan ne gida na. Abuja ya zama sabon gari na, kuma gwamna na shi ne Ministan harkokin birnin tarayya Abuja.”
“A nan (Abuja) na ke zama, kuma a nan ne nake yin ayyuka na.” - Chibuike Rotimi Amaechi.
Ministan sufuri
Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

APC: Amaechi da shirin 2023 a Ribas

Da aka nemi jin ta bakin Amaechi ko yana da shirin ya koma gida, sai ya ce idan lokaci ya yi, zai tsallaka, amma zuwa yanzu Ministan Abuja ne gwamnansa.

Da yake amsa tambayoyi, Ministan mai-ci ya yarda yana jin tsoron magajinsa watau Nyesom Wike.

“Eh, ina matukar tsoron shi. Ina jin tsoron shi kwarai da gaske.” - Rotimi Amaechi

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya karyata Gwamna Fayemi, ya fadi sirrin da Shugaban kasa ya fada masu

Tsoron tsiya gare ni - Rotimi Amaechi

Da ‘dan jarida ya nemi jin abin da ya sa Amaechi a matsayinsa na tsohon gwamna zai rika dari-darin gamuwa da Wike, sai ya yi masa gatse, ya na dariya.

“Saboda ni mutum ne mai ‘dan karen tsoro mana! Mecece matsalarka? Idan mu ka isa bakin gabar gada, za mu tsallaka gadar.” – Hon. Rotimi Amaechi

Wike zai yi takara a PDP

A jiya ne aka ji cewa Gwamna Nyesome Wike ya kaddamar da shirin neman takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa, ya ce PDP ce za ta lashe zabe a kasar nan.

Da yake kaddamar da takarar ta sa, Nyesom Wike ya yi wa su Atiku Abubakar, Bukola Saraki da Aminu Tambuwal shagube a kan ficewa daga jam'iyyar PDP a 2014.

Asali: Legit.ng

Online view pixel