Gwamnan Arewa ya karyata Gwamna Fayemi, ya fadi sirrin da Shugaban kasa ya fada masu

Gwamnan Arewa ya karyata Gwamna Fayemi, ya fadi sirrin da Shugaban kasa ya fada masu

  • Goyon bayan da Abdullahi Adamu ya samu daga fadar shugaban kasa ya jawo sabani a gidan APC
  • Wasu daga cikin jagororin jam’iyyar APC mai mulki ba su goyon bayan Sanata Abdullahi Adamu
  • Gwamnan jihar Ekiti yana ganin ba a za a janyewa ‘Yan takarar Mai girma shugaban kasa a zaben ba

Abuja - Daily Trust ta ce kokarin dinke baraka ya sa Muhammadu Buhari ya yi zama na musamman da gwamnoni a ranar Laraba domin kai ya hadu.

Matsayar da aka tashi bayan zaman makon nan shi ne gwamnoni za su goyi bayan takarar Abdullahi Adamu, amma sai aka ji magana ta na neman canzawa.

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya fito yana cewa babu wannan maganar, kuma za a gwabza ne wajen samun kujerun majalisar NWC na jam’iyyar ta APC.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Fayemi ya yi watsi da batun goyon bayan yan takarar da Buhari ke so

Dr. Kayode Fayemi ya ce shi bai da labarin akwai ‘yan takarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke marawa baya, ya ce ko ya abin yake sai an shiga zabe.

“Ba ni da masaniya a kan wannan. Amma shugaban kasa yana da damar da zai so wani ‘dan takara…idan ‘dan takararsa ya yi nasara to, idan bai yi ba, shikenan.”

- Dr. Kayode Fayemi

Lalong ya sha bam-bam da Fayemi

Amma da aka yi hira da Mai girma gwamna Simon Lalong na jihar Filato a gidan talabijin na Channels TV, ya shaida cewa Buhari ya fada masu ra’ayinsa.

Shugaban kasa
Shugaban kasa tare da jagororin APC Hoto: @bashahmad
Asali: Facebook

Gwamna Simon Lalong ya ce shugaban kasa bai boye cewa yana tare da Abdullahi Adamu ba.

Abin da dokar zabe ta ce inji Lalong

Kara karanta wannan

Shugabancin APC: Dalilin da yasa muka miƙa wuya ga ɗan takarar da Buhari ke kauna, Gwamna ya fasa kwai

Lalong ya ce ya saurari maganar da wasu su ke yi, ya yi masu karin haske da cewa dokar zabe da tsarin mulki sun yarda a fito da ‘yan takara ne ta hanyoyi uku.

Akwai tsarin zaben kato bayan kato, akwai na zaben ‘yan jam’iyya, sannan akwai maslaha, Lalong ya ce a wannan tsarin jam’iyyar APC ta ke tafiya a kai.

Sanata Abdullahi Adamu ne!

Da aka tambaye Lalong ko wa shugaban kasan yake goyon baya, sai ya ce yanzu kowa ya fahimci wanene shi. Maganar Sanata Abdullahi Adamu ake yi kenan.

“Gwamnoni sun tambayi Buhari ko ya na da ‘dan takara, sai ya ce zai so ne a samu wanda ya fito daga yankin Arewa maso tsakiya.”
“Sai mu ka sake komawa mu ka tambaya ko yana da wani a ransa, sai ya ce ‘Eh, zan fi son Abdullahi Adamu.’” – Gov. Lalong

Buhari ya gana da iyayen APC

Kara karanta wannan

Babu yadda gwamnonin APC suka iya, sun goyi bayan wanda Buhari ke so a zaben jam'iyya

A jiya da yamma aka ji mutane 11 ne aka yi wani muhimmin zama da su yayin da sa’o’i suka ragewa jam’iyyar APC mai mulki ta zabi sababbin shugabanninta.

Bola Tinubu, Bisi Akande, Rochas Okorocha, Ibrahim Shekarau da wasu Ministoci da Gwamnoni su na cikin wadanda aka rufe kofa da su a fadar Shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel