Taron APC: Jerin sunayen sabbin zababbun shugabannin APC na kasa 77

Taron APC: Jerin sunayen sabbin zababbun shugabannin APC na kasa 77

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta gudanar da babban taronta daga ranar 26 zuwa 27 ga watan Maris, gabannin babban zaben 2023.

A yayin taron, an zabi jami’an jam’iyyar na kasa su 77, inda Abdullahi Adamu ya zama shugaban jam’iyyar na kasa.

Adamu ya zama shugaban ne bayan sauran yan takarar kujerar shida sun janye.

Sun zama shugabannin ne a daren ranar Asabar ta hanyar yarjejeniya bayan gwamnonin jam’iyyar sun fitar da sunayen.

Taron APC: Jerin sunayen sabbin zababbun shugabannin APC na kasa 77
Taron APC: Jerin sunayen sabbin zababbun shugabannin APC na kasa 77 Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Ga cikakken sunayen sabbin shugabannin na kasa 77 bayan babban taronsu na 2022:

1. Shugaban jam’iyya na kasa – Sanata Abdullahi Adamu (Jihar Nasarawa).

2. Mataimakin Shugaban jam’iyya na kasa (Arewa): Sanata Abubakar Kyari (Jihar Borno).

3. Mataimakin Shugaban jam’iyya na kasa (Kudu) Emma Eneukwu (Jihar Enugu).

4. Sakataren jam’iyya na kasa: Otunba lyiola Omisore (Jihar Osun).

5. Mataimakin Sakataren jam’iyya na Kasa: Fetus Fuanter (Jihar Filato).

6. Mataimakin shugaban jama’iyya na kasa (Arewa Ta Tsakiya): Muhazu Bawa Rijau (Jihar Neja).

7. Mataimakin shugaban jama’iyya na kasa (arewa maso gabas): Mustapha Salihu (Jihar Adamawa)

8. Mataimakin shugaban jama’iyya na kasa (arewa maso yamma): Salihu Lukman (Jihar Kaduna)

9. Mataimakin shugaban jama’iyya na kasa (kudu maso gabas): Dr. Ijeomah Arodiogbu (Jihar Imo)

10. Mataimakin shugaban jama’iyya na kasa (kudu maso kudu): Cif Hon. Victor Ton Giadom (Jihar Rivers)

11. Mataimakin shugaban jama’iyya na kasa (kudu maso yamma): Dr Isaac Kekemeke (Jihar Ondo)

12. Mai ba jam’iyya shawara kan harkokin shari’a: Ahmed El-Marzuk (Jihar Katsina)

13. Ma’ajin jam’iyya na kasa: Uguru Mathew Ofoke (Jihar Ebonyi)

14. Sakataren kudin jam’iyya na kasa: Bashir Usman Gumel (Jihar Jigawa)

15. Sakataren kula da tsare-tsaren jam’iyya na kasa: Suleiman M Argungu (Jihar Kebbi)

16. Shugaban matasan jam’iyya na kasa: Dayo Abdullah Isreal (Jihar Lagas)

17. Sakataren kula da jin dadin jam’iyya na kasa: F.N. Nwosu (Abia)

18. Sakataren yada labarai na jam'iyya na kasa: Felix Morka (Delta)

19. Mai binciken kudi na jam'iyya na kasa: Sanata Abubakar Malkafi (Bauchi)

20. Shugabar Matan jam'iyya na kasa: Dr. Betta Edu (Cross River)

21. Shugaban nakasassun jam’iyya: Tolu Bankole (ogun)

22. Mataimakin mai ba jam'iyya shawara kan harkokin shari'a na kasa: Ibrahim Salawu (kwara)

23. Mataimakin ma’ajin jam’iyya na kasa: Omorede Osifo (Edo)

24. Mataimakin sakataren kudin jam’iyya na kasa: Hamma-Adama Ali Kumo (Gombe)

25. Mataimakin sakataren kula da tsare-tsaren jam’iyya na kasa: Nze Chidi Duru (Anambra)

26. Mataimakin sakataren yada labarai na jam'iyya na kasa: Yakubu Murtala Ajaka (Kogi)

27. Mataimakin Sakataren kula da jin dadin jam’iyya na kasa: Dr Christopher Akpan( Akwa Ibom)

28. Mataimakin mai binciken kudi na jam'iyya na kasa: Olufemi Egbedeyi (Oyo)

29. Mataimakiyar shugabar Matan jam'iyya na kasa: Zainab Abubakar Ibrahim (Taraba)

30. Mataimakin shugaban matasan jam’iyya na kasa: Jamaludden Kabir (Zamfara)

31. Mamban ofishin shiyya (arewa ta tsakiya): Oluwatoyin Opawuye (Kwara)

32. Mamban ofishin shiyya (arewa maso gabas): Sirajo Dabuwa (Bauchi)

33. Mamban ofishin shiyya (arewa maso yamma): Aliyu Ahmed Yako (Kano)

34. Mamban ofishin shiyya (kudu maso gabas): Agunwa Anekwe( Anambra)

35. Mamban ofishin shiyya (kudu maso kudu): Diriwari Akedewei (Bayelsa)

36. Mamban ofishin shiyya (kudu maso yamma): Mrs Bunmi Oriniowo (Ekiti)

37. Sakataren Shiyya (Arewa Ta Tsakiya): Yakubu Mohammed Adamu (FCT)

38. Sakataren Shiyya (Arewa maso Gabas): Mohammed Wali Shettima (Yobe)

39. Sakataren Shiyya (Arewa maso Yamma): Barista Bello Goronyo (Sokoto)

40. Sakataren Shiyya (Kudu maso Yamma): Vincent Bewaji (Ekiti)

41. Sakatariyar shiyyar (Kudu maso Gabas): Azobi Innocent Itapi (Ebonyi)

42. Sakataren Shiyya (Kudu maso Kudu): Dr Ita Udosen (Akwa Ibom)

43. Mai bada shawara kan Shari’a na shiyya (arewa maso gabas): Dauda Chapo (Taraba)

44. Mai bada shawara kan Shari’a na shiyya (arewa ta tsakiya): Hadiza Aliyu(Kogi)

45. Mai bada shawara kan Shari’a na shiyya (arewa ta yamma):Barr.Dauda Usaini Dutse( Jigawa)

46. Mai bada shawara kan Shari’a na shiyya (Kudu maso Gabas): Magajin Garin Ogbona Ernest(Ebonyi)

47. Mai bada shawara kan Shari’a na shiyya (Kudu maso Kudu):

49: Sakataren tsare-tsare na shiyya (arewa maso gabas): Abubakar Adamu Musa( Taraba)

50. Sakataren tsare-tsare na shiyya (arewa maso yamma): Salisu Uba (Zamfara)

51. Sakataren tsare-tsare na shiyya (arewa ta tsakiya): Ahmed Attah (Kogi)

52. Sakataren tsare-tsare na shiyya (kudu maso yamma): Lateef Ibirogba

53. Sakataren tsare-tsare na shiyya (kudu maso gabas): Dozie Ikadite (Anambra)

54. Sakataren tsare-tsare na shiyya (kudu maso kudu): Blessing Agboma (Edo)

55. Sakataren yada labarai na shiyya (Arewa maso Gabas): Lamido Mohammed (Gombe)

56. Sakataren yada labarai na shiyya (Arewa ta tsakiya): John Okobo (Benue)

57. Sakataren yada labarai na shiyya (Arewa maso yamma): Musa Makatiya (Zamfara)

58. Sakataren yada labarai na shiyya (kudu maso gabas): Augustine Onyedebehi(Imo)

59. Sakataren yada labarai na shiyya (Kudu maso Kudu)

60. Sakataren yada labarai na shiyya (kudu maso yamma): Ayo Afolabi

61. Shugabar mata na shiyya (Arewa ta tsakiya): Oluwatoyin Opawuye (Kwara)

62. Shugabar mata ta shiyya (Arewa maso Gabas): Zainab Abubakar Alman (Gombe)

63. Shugabar mata ta shiyya (arewa maso yamma): Hajiya Hadiza Shagari( Sokoto)

64. Shugabar mata ta shiyya (kudu maso yamma): Mrs Yetunde Adesanya (Ogun)

65. Shugabar mata ta shiyya (kudu maso kudu): Caroline Owugha (Bayelsa)

66. Shugabar mata ta shiyya (kudu maso gabas): Mimi Uchenna Diyokeh (Enugu)

67. Shugaban matasan shiyya (arewa ta tsakiya): Zubairu Aliyu (Kwara)

68: Shugaban matasan shiyya (Arewa maso yamma): Abdulhamid Umar Mohammed (Kano)

69. Shugaban matasan shiyya (Arewa maso Gabas): Jason Baba Kkwaghe (Adamawa)

70. Shugaban matasan shiyya (kudu maso gabas): Nkenna Anyalewechi (Abia)

71. Shugaban matasan shiyyar (Kudu maso yamma): Kolade Lawal (Ondo)

72. Shugaban matasan shiyya (Kudu maso Kudu): Comrade Ebimobowe (Delta)

73: Shugaban nakasassu na shiyya (arewa ta tsakiya): Laho Lazarus Audu (Benue)

74. Shugaban nakasassu na shiyya (arewa maso Gabas): Mohammed Baba Isa (Yobe)

75. Shugaban nakasassu na shiyya (Arewa maso Yamma): Lawal Na Rago (Kano).

76. Shugaban nakasassu na shiyya (Kudu maso Kudu): Cif Edet Aziz ( Cross River)

77. Shugaban nakasassu na shiyya (kudu maso gabas): Dr Nwachukwu Stanley Chinedu (Imo)

Babban taron APC: Bidiyon shugaba Buhari yayin da ya isa wajen rantsar da shugabannin APC na kasa

A gefe guda, mun ji cewa an rantsar da kwamitin shugabancin APC na kasa karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu.

An rantsar da Adamu da sauran mambobin kwamitin a ranar Lahadi, 26 ga watan Maris, yayin gangamin taron jam’iyyar mai mulki a Eagles Square da ke Abuja.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin shugaban kasa da sauran manyan shugabannin jam’iyar sun halarci taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel